Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari, Sun Kashe Malami Tare da Sace Bayin Allah Sama da 35

Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari, Sun Kashe Malami Tare da Sace Bayin Allah Sama da 35

  • Yan bindiga sun kai hari garuruwa uku a birnin tarayya Abuja da jihar Neja da ke maƙotaka, sun kashe mutane huɗu
  • Rahotanni sun nuna cewa yayin hare-haren a lokuta daban-daban, yan ta'addan sun yi garkuwa da wasu mutane 39
  • Daga cikin waɗanda maharan suka kashe harda malamin cocin RCCG, wanda suka shiga har gida suka harbe shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Miyagun ƴan bindiga sun halaka rayukan mutum huɗu kuma sun yi garkuwa da wasu akalla 39 a hare-haren da suka kai wasu garuruwa a Abuja da jihar Neja.

Vanguard ta tattaro cewa ƴan bindiga sun kai farmaki ne garin Kuduru da ke yankin Bwari a Abuja da kuma kauyukan Garam da Azu duk a jihar Neja.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe yan sanda, sun sace fasinjojin da suka tafi hutun Kirsimeti

Sufetan yan sandan Najeriya.
Yan Bindiga Sun Kashe Rayuka 4, Sun Sace Mutane 39 a Abuja da Jihar Neja Hoto: PoliceNG
Asali: Twitter

Yadda yan bindigan suka shiga garuruwa 3

Ganau sun bayyana cewa tsagerun ƴan ta'addan sun kutsa kai cikin kauyen Garam a jihar Neja ranar Asabar 23 ga watan Disamba, bai wuce minti 5 ba zuwa Bwari a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin harin, sun kashe malamin coci wanda aka fi sani da Fasto a Redeemed Christian Church of God (RCCG), kana suka yi garkuwa da wasu ƙarin mutum 13.

A ranar Alhamis 28 ga watan Disamba, ‘yan bindigar suka sake kai hari garin Kuduru a FCT, wanda ke kan iyaka da Garam, inda suka yi garkuwa da mutane 18.

Washe gari, ranar Juma’a 29 ga watan Disamba, ‘yan bindiga suka mamaye garin Azu na jihar Neja, inda suka kashe mutane uku tare da yin garkuwa da wasu takwas.

Wata mazauniyar Garam, wacce ta bayyana kanta da Misis Juliana ta ce da farko ‘yan bindigar sun rasa abin harinsu, suka shiga gidan da ba shi suka nufa ba, inda suka yi awon gaba da yara biyu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun halaka bayin Allah sama da 100 a jihar arewa, sun tafka mummunar ɓarna

A rahoton Daily Post, matar ta ce:

"Da farko sun yi kuskuren shiga wani gida, suka ɗauki yara maza guda biyu waɗanda daga bisani suka yi musu jagora zuwa gidan da suke nema."
"Daga zuwa suka tattara mutanen gidan gaba ɗaya suka tafi da su, sai da zasu tafi ne sai suka harbe asalin wanda suka zo dominsa, wani Fasto a cocin RCCG."

'Yan bindiga sun buɗe wa ayarin jagoran PDP wuta

A wani rahoton na daban Yan bindiga sun kashe 'yan sanda biyu yayin da suka kai hari kan ayarin jagoran PDP a jihar Anambra, Chris Uba.k

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun buɗe wa ayarin wuta ranar Alhamis da daddare amma jigon siyasan ya sha da ƙyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262