Rundunar Sojojin Najeriya Ta Kama Jami’inta Kan Mutuwar Direban Babban Mota a Borno
- Wani jami'in soja da ake zargi da kisan wani direban babban mota a hanyar Gamboru-Dikwa da ke Maiduguri jihar Borno, ya shiga hannu
- Rundunar sashi na 7 ta tabbatar da kama jami'in nata tare da kaddamar da bincike kan zargin kisan
- Gwamnatin jihar Borno ta sha alwashin bin diddigin al'amarin tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu a ciki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Maiduguri, Jihar Borno - Rundunar sashi na 7 na sojojin Najeriya da ke Maiduguri ta ce ta kama wani jami'in soja da ake zargi da hannu a mutuwar wani direban babban mota a hanyar Gamboru-Dikwa.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa a cikin wata sanarwa da ya yi a ranar Alhamis, 28 ga watan Disamba, A.Y. Jingina, kakakin rundunar, ya ce lamarin ya afku ne a washegarin ranar Kirismeti a wani shingen bincike inda aka tura sojoji aiki.
Ya bayyana cewa an kama sojan da abun ya shafa kuma tuni aka fara gudanar da bincike a kan lamarin, rahoton The Cable
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jingina ya ce bayan afkuwar lamarin, kungiyar ta kulla yarjejeniya da kungiyar ma’aikatan sufurin mota ta kasa (NURTW) domin dakile wani rikici.
Ya ce:
“Rashen ya tabbatar wa iyalan marigayin da kuma kungiyar NURTW jajircewarsa don ganin an yi wa iyali adalci kuma ba za a yi rufa-rufa a lamarin ba.
"Rundunar na son sake tabbatar wa da jama'a cewa za mu ci gaba da jajircewa da nuna kwarewa a kokarin hadin gwiwa da muke yi na magance matsalar rashin tsaro a jihar Borno."
Gwamnatin Borno ta yi martani
Usman Tar, kwamishinan yada labarai na jihar, ya ce za a yi "binciken da ya dace" kuma gwamnati za ta tabbatar da adalci.
Ya bayyana a cikin sanarwar da ya fitar cewa
“Gwamnati na bin bibiyar wannan al’amari kuma za ta dauki duk matakan da suka kamata don ganin an yi bincike yadda ya kamata kan lamarin tare da gurfanar da wadanda ake zargi a kotu. Duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci fushin doka.
“A halin da ake ciki, gwamnatin jihar Borno tana kira ga jama’a musamman ma ‘yan kungiyar ma’aikatan sufuri da su kasance masu hakuri da kamala yayin da ake tafiyar da lamarin kamar yadda doka ta tanada."
Ana barazanar kai hari Filato
A wani labarin, mun ji cewa a daidai lokacin da al’umma ba ta gama makokin dinbin mutanen da aka kashe a Filato ba, an ji ana neman sake kai wani harin.
Kungiyar Middle-Belt Forum (MBF) ta mutanen tsakiyar Najeriya ta ce an rubuta takardar kawo hari, labarin ya zo a jaridar nan ta Vanguard.
Asali: Legit.ng