Na'Abba: Tsohon Shugaban Majalisa Ya Fadi Yadda Suka Shirya Taimakon Marigayin Kafin Ya Rasu
- Anyim Pius Anyim ya jajantawa iyalan tsohon kakakin Majalisar Wakilai, Ghali Umar Na'Abba
- Anyim wanda tsohon shugaban Majalisar Dattawa ne ya nuna alhininsa kan rasuwar inda ya ce ya rasu a lokacin da suke shirin taimakonshi
- Wannan na zuwa ne bayan rasuwar marigayin a jiya Laraba 27 ga watan Disamba a wani asibiti da ke Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Anyim Pius Anyim ya bayyata kaduwarshi kan rasuwar Ghali Umar Na'Abba a Abuja.
Anyim ya ce sun kammala shirin taimakawa tsohon kakakin Majalisar Wakilai kwanaki kadan kafin rasuwarshi.
Mene Pius Anyim ke cewa kan marigayi Na'Abba?
Jimami yayin da babban mai sarautar gargajiya ya rasu ya na da shekaru 61 a duniya, bayanai sun fito
Ya ce da shi da tsaffin jagororin Majalisar sun yi zama a ranar 23 ga watan Disamba inda suka ce za su koma asibitin Abuja don daukar mataki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Pius ya ce sun yi shawarar daukar nauyin Na'Abba zuwa kasr waje don samun lafiya cikin gaggawa, cewar Tribune.
Ya ce:
"Abin bakin ciki a ranar 27 ga watan Disamba mummunan labarin rasuwarshi ta yadu wanda bai bamu damar taimaka masa ba."
Wane sako Anyim Pius ya tura ga iyalan Na'Abba?
Ya kara da cewa:
"Tabbas mutuwar Ghali babban rashi ne ga al'ummar Najeriya da kasar da ma mulkin dimukradiyya a kasar."
Tsohon shugaban Majalisar ya bayyana haka ne a yau Alhamis 28 ga watan Disamba yayin mika sakon jaje ga iyalan marigayin, Newsngr ta tattaro.
Anyim a madadin tsaffin jagororin Majalisun biyu ya mika sakon ta'aziya ga iyalan marigayin da kuma kasar Najeriya baki daya.
Ghali Na'Abba ya riga mu gidan gaskiya
A wani labarin, a ranar Laraba ce 27 ga watan Disamba aka wayi gari da mummunan labarin rasuwar tsohon kakakin Majalisar Wakilai, Ghali Umar Na'Abba.
Marigayi Ghali ya rasu ne a wani asibiti da ke birnin Abuja bayan fama da jinya na tsawon lokaci.
Daga bisani an dauki gawar shi zuwa birnin Kano inda aka yi sallar jana'izarsa da misalin karfe 5:38 na yamma.
Asali: Legit.ng