Jimami Yayin da Babban Mai Sarautar Gargajiya Ya Rasu Ya Na da Shekaru 61 a Duniya, Bayanai Sun Fito
- An shiga jimami bayan rasuwar mai sarautar gargajiya a kauyen Umunya da ke karamar hukumar Oyi a jihar Anambra
- Marigayin Chris Onyekwuluje da ke sarautar yankin Umunya ya rasu ya na da shekaru 61 bayan fama da jinya
- Shugaban yankin, Cif Innocent Nwabueze ya bayyana mutuwar masaraucin gargajiyar a matsayin abin takaici
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Anambra – Babban mai sarautar gargajiya a jihar Anambra ya rigamu gidan gaskiya a yau Alhamis 28 ga watan Disamba.
Marigayin Chris Onyekwuluje da ke sarautar yankin Umunya a karamar hukumar Oyi da ke jihar ya rasu ya na da shekaru 61.
Yaushe mai sarautar gargajiyar ya rasu?
Chris wanda ya hau karagar mulkin kauyen ne shekaru 25 da suka wuce inda ya rasu a birnin Abuja bayan fama da jinya, cewar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban yankin, Cif Innocent Nwabueze ya bayyana mutuwar masaraucin gargajiyar a matsayin abin takaici.
Ya ce:
“Dole mu karbi wannan lamari da gaskiya, shugabanmu ya tafi, yaushe zai dawo wannan ba mu sani ba, amma abin bakin ciki ne a gare mu.”
Rahotanni sun tabbatar da cewa marigayin ya rasu ne bayan fama da jinyar ciwon daji na tsawon lokaci, cewar Platinum Post.
Wata majiya ta ce:
“Duk da bai yi wani abin banza a kauyen ba, amma mutuwarshi ba wanda za a yada a kafafen sadarwa ba ce.
“Kauyen Umunya ta na da tsarin sanar da dukkan wata mutuwa musamman da masu sarautar gargajiya.”
Marigayin ya sanu musamman a lokacin mulkin tsohon gwamnan jihar Anambra, Chinwoke Mbadinuju.
A kwanakin nan ya fada wa mutanen kauyen cewa zai mulke su har na tsawon shekaru 100.
Wannan furuci na shi ya fusata dattawan yankin wadanda suka nuna fushinsu a fili kan kalaman marigayin.
Tsohon gwamna Akeredolu ya rasu
A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ya rasu a jiya Laraba 27 ga watan Disamba.
Akeredolu ya rasu ne a kasar Jamus bayan fama da jinya ta cutar daji na tsawon lokaci a Jamus.
Daga bisani, an rantsar da mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa da misalin karfe hudun ranar Larabar a birnin Akure.
Asali: Legit.ng