“Na Hakura”: Kwamishinan Akeredolu Ya Yi Murabus Bayan Aiyedatiwa Ya Zama Gwamnan Ondo

“Na Hakura”: Kwamishinan Akeredolu Ya Yi Murabus Bayan Aiyedatiwa Ya Zama Gwamnan Ondo

  • Kasa da awanni 24 da rantsar da Lucky Aiyedatiwa matsayin sabon gwamnan jihar Ondo, wani kwamishinan jihar ya ajiye aikinsa
  • Kwamishinan gine-gine, filaye da gidaje na jihar, Raimi Aminu ya yi murabus a ranar Alhamis 28 ga watan Disamba, 2024
  • A cewar Aminu, babu amfanin ci gaba da rike mukamin bayan mutuwar shugabansa, Rotimi Akeredolu (gwamnan jihar kafin mutuwarsa)

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Ondo - Kwamishinan gine-gine, filaye da gidaje na jihar Ondo, Raimi Olayiwola Aminu, ya yi murabus daga mukaminsa.

Wannan na zuwa kasa da awanni 24 bayan da aka rantsar da Lucky Aiyedatiwa matsayin sabon gwamnan jihar Ondo biyo bayan mutuwar Oluwarotimi Akeredolu.

Kwamishinan jihar Ondo ya yi murabus
Kwamishinan gine-gine, filaye da gidaje na jihar Ondo, Raimi Olayiwola Aminu, ya yi murabus daga mukaminsa. Hoto: Lucky Orimisan Aiyedatiwa
Asali: Facebook

Kwamishina ya yi murabus bayan mutuwar Akeredolu

Kara karanta wannan

Aiyedatiwa: Jerin hadiman gwamna da suka yi murabus daga muƙamansu bayan mutuwa ta gitta

Aminu, a cikin wata wasika da ya aike wa sakatariyar gwamnatin jihar, Princess Oladunni Odu, ya ce ajiye aikinsa zai fara aiki ne daga ranar Alhamis, 28 ga watan Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aminu ya ce ya ajiye aikin ne saboda shugabansa Arakunrin Oluwarotimi Odunayo Akeredolu ya amsa kiran ubangiji, bai ga dalilin ci gaba da rike mukamin ba, The Nation ta ruwaito.

A cewar sa:

"Ina matukar godiya ga Arakunrin da mutane jihar Ondo bisa damar da suka bani na yi wa jihar hidima matsayin babban hadimin gwamna kan filaye da gine-gine.
"Babban mashawarci ga gwamnan kan filaye, ayyuka da gine-gine, da kuma aiki a matsayin kwamishinan gine-gine, filaye da gidaje na jihar."

An rantsar da Lucky Aiyedatiwa matsayin gwamnan Ondo

A wani labarin, Lucky Aiyedatiwa ya karbi rantsuwar kama aiki matsayin sabon gwamnan jihar Ondo bayan mutuwar Rotimi Akeredolu a ranar Laraba, 27 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

"Ba daɗi" Ɗan marigayi Akeredolu ya bayyana gaskiyar yadda gwamnan APC ya mutu, abun tausayi

Kafin zamansa gwamna, shi ne mataimakin gwamnan jihar, kuma mukaddashin gwamna na tsawon makonni biyu bayan tafiyar Akeredolu Jamus neman magani.

Manyan jiga-jigan da suka halarci bikin rantsarwan sun haɗa da kakakin majalisar dokoki, Olamide Oladiji, sakataren gwamnatin jiha, Oladunni Odu da wasu mambobin majalisar zartarwa.

Gwamna Akeredolu ya riga mu gidan gaskiya

A ranar Laraba ne Legit Hausa ta ruwaito maku rasuwar gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, wanda ya rasu yana da shekaru 67 a duniya.

Akeredolu ya yi fama da rashin lafiyar sankarar bargo da mafitsara, inda ya je kasashe daban-daban nema lafiya, amma karshe rashin lafiyar ta tsananta, har ya koma ga ubangiji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.