“Akwai Sa Hannun Wasu Mutane a Mutuwar Akeredolu”, Sowore Ya Yi Zargi

“Akwai Sa Hannun Wasu Mutane a Mutuwar Akeredolu”, Sowore Ya Yi Zargi

  • Dan siyasa kuma mai rajin kare hakkin dan adam, Omoyele Sowore, ya bayyana cewa babu dalilin dawo da Rotimi Akeredolu Najeriya daga Jamus
  • Jaridar Legit ta rahoto cewa har zuwa mutuwarsa a safiyar Laraba, 27 ga watan Disamba, Akeredolu ya kasance gwamnan jihar Ondo
  • Tsohon gwamnan ya rasu yana da shekaru 67, bayan ya yi fama da cutar kansa tare da kai shi kasar waje don yin magani fiye da sau daya

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Akure, jihar Ondo - Omoyele Sowore, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar AAC a zabukan 2019 da 2023, ya ce wasu mutane na da hannu a mutuwar tsohon gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu.

Da yake magana a wata hira da News Central a ranar Laraba, 27 ga watan Disamba, wanda jaridar Legit ta bibiya, Sowore ya ce idan da a wurin dake aiki da hankali ne, da za a gurfanar da wadanda ke da hannu a mutuwar Akeredolu.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da sabon gwamnan jihar Ondo, Aiyedatiwa

Rotimi Akeredolu
“Wasu Mutane Na da Hannu a Mutuwar Akeredolu”, Sowore Ya Yi Zargi Hoto: Rotimi Akeredolu Aketi
Asali: Facebook

"Babu dalilin kawo Akeredolu Najeriya"

Tsohon gwamnan na jihar Ondo ya mutu a kasar Jamus a ranar Laraba, 27 ga watan Disamba, bayan ya yi fama da cutar kansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake martani kan mutuwar tsohon gwamnan, Sowore ya ce ba don rikicin mulki wanda ya kunshi Betty Anyanwu-Akeredolu ba, da kamata ya yi ace Akeredolu ya ci gaba da kasancewa a Jamus domin kula da lafiyarsa da kyau.

Sowore ya ce:

"Abun bakin ciki ne cewa iyalinsa da wasu yan siyasa suka yi masa haka. Babu dalilin kawo shi daga Jamus zuwa Najeriya - kawai saboda siyasa. Kuma watakila wannan ya kawo mutuwarsa cikin gaggawa. Amma duk da haka, cutar kansa ba abu ne da za ka yi wa wani fata ba, musamman idan ya kai matakin karshe, lokaci ne kawai.
"Magana ta gaskiya daga abun da na ji kuma na sani, an ba shi zuwa watan Mayun 2023 ne, inda ya dan kara lokaci kadan. Shakka babu, da zai kara tsawon lokaci idan da matarsa (Betty) bata tursasa masa dawowa da yin amfani da kasancewarsa wajen tsige mataimakinsa (Lucky Aiyedatiwa) ba, wanda a yau shine gwamnan jihar."

Kara karanta wannan

Aiyedatiwa: An rantsar da sabon gwamnan Ondo bayan mutuwar Gwamna Akeredolu, bayanai sun fito

Kalli bidiyon Sowore a kasa:

Gwamnatin Ondo ta sanar da mutuwar Akeredolu

A baya mun ji cewa cikin jimami da kaɗuwa, Gwamnatin jihar Ondo ta sanar da rasuwar Gwamna Oluwarotimi Akeredolu (SAN) a hukumance.

Gwamna Akeredolu na jam'iyyar APC ya cika ne da safiyar ranar Laraba, 27 ga watan Disamba, 2023 bayan fama da doguwar jinya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: