Shugaba Tinubu Ya Nuna Alhini Kan Rasuwar Ghali Na'Abba, Ya Aike da Sako Mai Muhimmanci
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa kan rasuwar Ghali Umar Na'Abba, tsohon kakakin majalisar wakilai
- A ranar Laraba 27 ga watan Disamba ne tsohon ɗan majalisar wanda haifaffen jihar Kano ne ya rasu a Abuja
- Shugaba Tinubu, a cikin yabon da ya yi masa, ya bayyana shi a matsayin “ɗan siyasa mai tarbiyya da jajircewa” a zamaninsa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar Kano biyo bayan rasuwar Ghali Umar Na’Abba, tsohon kakakin majalisar wakilai.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, 27 ga watan Disamba, ta hannun mai bai shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale, Tinubu ya bayyana marigayi Na’Abba a matsayin “Ɗan siyasa mai ɗa’a da jajircewa."
Shugaba Tinubu ya nuna alhininsa bisa rasuwar, inda ya yi nuni da irin gudunmawar da marigayi tsohon ɗan majalisar ya bayar wajen gina ƙasa ta hanyar gudanar da ayyukan majalisa, shawarwari da tsare-tsare.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban ya tuna da irin namijin ƙoƙarin da Na’Abba ya yi na tabbatar da inganci da muhimmancin majalisa wajen gudanar da mulki, inda ya yaba masa a matsayinsa na ɗan siyasa mai ƙwazo da tsayawa tsayin daka.
Shugaba Tinubu ya nuna alhininsa
Shugaba Tinubu ya yi addu’ar samun rahama ga marigayin da kuma ta’aziyya ga waɗanda ke cikin wannan rashi mai raɗaɗi.
Marigayi Na'Abba shi ne kakakin majalisar wakilai bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a Najeriya daga 1999 zuwa 2003, inda ya gaji Salisu Buhari.
Na’Abba ya samu yabo saboda rawar da ya taka a matsayin Shugaban Majalisar.
Wannan karramawar ta samo asali ne daga jarumtakarsa, jajircewarsa, jagoranci mai fa'ida, jajircewarsa na ƴancin cin gashin kai na majalisa, da sabbin tsare-tsare na majalisar a zamaninsa.
Ganduje Ya Yi Ta'aziyyar Ghali Na'Abba
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya aike da saƙon ta'aziyyar Ghali Umar Na'Abba.
Tsohon gwamnan na jihar Kano, ya bayyana mariyagin a matsayin jajirtaccen ɗan siyasa wanda yake kishin ƙasar nan.
Asali: Legit.ng