Sabon Gwamnan Ondo, Aiyedatiwa Ya Isa Gidan Gwamnati Don Bikin Rantsar da Shi
- Rahotannin da ke fitowa daga jihar Ondo na nuni da cewa Lucky Aiyedatiwa ya isa gidan gwamnatin jihar don bikin rantsar da shi
- Tun da fari an saka karfe 4 na yamma matsayin lokacin da za a rantsar da Aiyedatiwa gwamnan jihar Ondo biyo bayan mutuwar Akeredolu
- A ranar Laraba 27 ga watan Disamba 2023 Gwamna Akeredolu ya mutu a kasar Jamus sakamakon cutar sankarar bargo da ta kama shi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Ondo - Mukaddashin gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya isa ofishin gwamnan domin bikin rantsar da shi a matsayin gwamnan jihar.
Za a rantsar da Aiyedatiwa a matsayin gwamnan jihar Ondo bayan rasuwar gwamna Oluwarotimi Akeredolu a ranar Laraba.
Rashin lafiyar Akeredolu da mika mulki ga Aiyedatiwa
Tafiyar da Aiyedatiwa ya yi na zama gwamnan jihar Ondo ya dau tsawon shekara guda tun bayan da Akeredolu ya sha fama da rashin lafiya kafin daga bisani ya mutu a kasar Jamus.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Aiyedatiwa ya tsallake rijiya da baya ne daga yunkurin tsige shi da wasu magoya bayan Akeredolu a majalisar dokokin jihar Ondo da kuma adawar da sha da sojojin bakar Akeredolu.
Rigima ta mamaye siyasar jihar a watannin baya inda masu fafutuka da lauyoyin tsarin mulki suka yi kira ga Akeredolu da ya mika mulki ga Aiyedatiwa kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar na 1999 ya tanada.
Daga karshe, Akeredolu, wanda ya zama gwamna a wa’adi na biyu kafin rasuwarsa, ya mika ragamar mulki ga Aiyedatiwa a ranar 13 ga Disamba, 2023.
Akeredolu, mai shekaru 67, ya kasa dawowa Najeriya da ransa yayin da ya mutu sakamakon kamuwa da cutar sankarar bargo, rahoton Channels TV.
Tinubu ya girgiza da mutuwar Rotimi Akeredolu
A wani labarin, Shugaba Tinubu ya kadu bayan rasuwar Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo a yau Laraba 26 ga watan Disamba.
Tinubu ya bayyana Akeredolu a matsayin jajirtacce wanda ya ba da gudunmawa wajen kwato mulki a shari'ar zaben jihohin APC.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin a bangaren yada labarai ta zamani, Bayo Onanuga ya fitar a yau Laraba 27 ga watan Disamba.
Asali: Legit.ng