Shugaban Gwamnonin Najeriya Ya Yi Magana Kan Rasuwar Gwamnan Jihar Ondo Na APC
- Shugaban NGF kuma gwamnan jihar Kwara ya yi ta'aziyyar rasuwar Gwamna Akeredolu na jihar Ondo
- Gwamma AbdulRazaq ya ce bayyana marigayin a matsayin dattijon ƙasa kuma wanda ba za a taɓa mantawa da shi ba
- Ya kuma yi ta'aziyya ga gwamnati da al'ummar jihar Ondo da kuma iyalansa, inda ya masa fatan samun salama
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kwara - Shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) kuma gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya yi magana kan rasuwar Gwamna Olurotimi Akeredolu (SAN) na jihar Ondo.
Shugaban gwamnonin ya bayyana alhini da jimamin rasuwar Gwamna Akeredolu, wanda Allah ya yi wa rasuwa bayan fama da doguwar jinya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna AbdulRazaq ya kuma aike da sakon ta'aziyya ga kungiyar gwamnonin APC, al'ummar jihar Ondo da kuma iyalan marigayin bisa wannan babban rashi.
Bugu da ƙari, ya yi ta'aziyya ga ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA) bisa rasuwar gwamnan, wanda ya kasance tsohon shugabanta, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Shugaban NGF ya tura sakon ta'aziyya
Ya bayyana marigayi gwamnan a matsayin dattijon ƙasa wanda ya yi abin da ba za a taba mantawa da shi ba a harkokin aikin gwamnati.
A kalamansa, Gwamna AbdulRazaq ya ce:
“Ina mika ta’aziyya ga kungiyar gwamnonin APC, gwamnati da al’ummar jihar Ondo, kungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA), da kuma dangin dan uwana kuma abokin aikina mai girma Olurotimi Akeredolu SAN."
"Lauya ne na sahun gaba kuma hazikin dan siyasa mai kishin ci gaba, za a tuna da shi bisa jajircewarsa, kishin kasa, da gudunmawar da ya bada mara misaltuwa ga tsarin mulki da cigaban siyasar Nijeriya."
"Duk da mutuwarsa ta sosa rai amma zamu rungumi haƙuri duba da kyawawan ayyukan da ya bari a matsayinsa na mai gaskiya kuma dattijon arziƙi."
Daga ƙarshe, shugaban NGF ya yi addu'ar Allah ya sa ransa a salama kuma ya kula da iyalan gwamnan, waɗanda ya mutu ya bari, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Abubuwan da ya kamata ku sani game da Gwamnan Ondo
A wani rahoton kuma bayan tabbatar da rasuwar gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu, Legit Hausa ta tattaro muku wasu muhimman abubuwa game da shi.
A ranar 13 ga watan Disamba ne Akeredolu ya dauki hutu don neman lafiyarsa inda Shugaba Tinubu ya ba da umurnin mika mulkin jihar hannun mataimakin Akeredolu, Mr Aiyedatiwa.
Asali: Legit.ng