Gwamnatin Tinubu Zata Ƙwace Wasu Bankuna a Najeriya Ta Kwashe kuɗin Mutane? Gaskiya Ta Bayyana
- Babban bankin Najeriya CBN ya musanta cewa FG zata kwace wasu bankuna kuma duk wanda ya ajiye kuɗi ya yi asara
- A wata sanarwa da CBN ya fitar ya tabbatarwa duk wani mai ajiya a bankunan Najeriya cewa kudinsa na cikin aminci da tsaro
- Wannan na zuwa ne yayin da ake raɗe-raɗin gwamnati zata kwace bankunan da ake zargin Emefiele ya mallake su a sirrince
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Babban bankin Najeriya (CBN) ya bai wa masu ajiya tabbacin cewa kudadensu na cikin tsaro a kowane banki suka ajiye a faɗin ƙasar nan.
Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun daraktan yaɗa labarai na CBN, Hakama Sidi-Ali, kuma bankin ya wallafa a shafinsa na twitter.
Babban bankin ya yi wannan karin haske ne domin musanta rahoton da wasu kafafen watsa labarai suka buga cewa gwamnati na shirin kwace wasu bankuna a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar rahotanni, Gwamnatin tarayya zata ƙwace bankunan ne bayan rahoton wanda aka ɗora ma alhakin bincknen CBN, Jim Obazee.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa Mista Obazee a matsayin wanda zai binciki harkokin CBN na musamman a watan Yuli, 2023.
A rahoton binciken da ya miƙa wa Tinubu, mai binciken ya yi zargin cewa tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya yi amfani da wakilai wajen mallakar bankuna 2.
Bayan samun wannan bayani ne aka fara yaɗa jita-jitar cewa gwamnatin tarayya ka iya kwace waɗan nan bankuna gaba ɗayansu.
Shin da gaske FG zata kwace bankuna 2?
A sanarwan, babban bankin ya yi bayanin cewa:
Kotun Koli na shirin yanke hukunci kan zaben Kano, Shugaba Tinubu ya aike da muhimmin saƙo ga Ganduje
"CBN ya lura da rahotanni da wasu kafafen yada labarai suka buga game da shawarin da aka ba gwamnatin tarayya na karbe wasu cibiyoyin hada-hadar kudi (bankuna) da CBN ke kula da su."
"Domin kare shanku da tantama, muna tabbatar muku da cewa bankuna na cikin tsaro. CBN na ƙara karfafawa al'umma guiwa su ci gaba da harkokinsu da bankuna ba tare da fargabar komai ba."
"Muna tabbatar wa jama'a da masu ajiya cewa kuɗaɗensu da ke bankuna suna cikin aminci. Saboda haka muna shawartan kwastomomin bankuna su ci gaba da mu'amala yadda suka saba."
Shugaba Tinubu zai shirya da Aregbesola
A wani rahoton kuma Malamin addinin Musulunci ya yi hasashen cewa shugaban ƙasa, Bola Tinubu da tsohon ministan cikin gida, Rauf Aregbesola, zasu sasanta da juna.
Babban malami a Ilorin, Sheikh Sulaiman Farooq Onikijapa, ne ya yi hasashen a wurin addu'ar takwas ta marigayi Sheikh Abdulwahab Banni Afonta.
Asali: Legit.ng