Jerin Abubuwa 5 Muhimmai da Ya Kamata Ku Sani Game da Marigayi Ghali Umar Na'Abba
FCT, Abuja - Da safiyar yau Laraba ce aka tashi da labarin rasuwar tsohon Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Ghali Umar Na'abba.
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Ghali ya rasu ne a wani asibiti da ke birnin Abuja bayan fama da jinya ya na da shekaru 65 a duniya.
Abubuwan da ya kamata ku sani
Daily Trust ta tattaro cewa marigayin kafin rasuwarshi ya yi gwagwarmaya wurin tabbatar da martabar dimukradiyya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit Hausa ta jero muku abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da marigayin.
1. Ranar haihuwarsa
An haifi Ghali Umar Na'abba a ranar 27 ga watan Satumbar shekarar 1958 a Tudun Wada da ke birnin Kano, cewar The Nation.
Mahaifinsa dan kasuwa ne kuma malamin addini wanda ya koya masa kasuwanci da hakuri da kuma rikon amana.
2. Ilimi
Marigayin ya fara da makarantar firamaren Jakara inda ya kammala a 1969 kafin ya wuce Kwalejin Rumfa inda ya samu satifiket a 1976.
Umar Na'abba ya samu damar shiga Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria inda ya karanta Kimiyyar Siyasa a 1979.
Har ila yau, ya karo ilimin shugabanci a Jami'ar Havard da ke Amurka a 2004.
3. Kasuwanci
Bayan kammala bautar kasa, marigayin ya fara aiki a kamfanin mahaifinsa a shekarar 1980.
Kamfanin ya kware wurin shigo da kayayyaki da kuma samar da su a cikin gida.
Ya fara a matsayin sakataren kamfanin kafin daga bisani ya zama babban manaja a kamfanin.
4. Siyasa
Tun a Jami'ar Ahmadu Bello aka zabe shi a matsayin mamban kwamitin jami'yyar PRP ta Mallam Aminu Kano a wancan lokaci.
Na'Abba ya shiga jam'iyyar PDP a 1998 inda ya tsaya takarar Majalisar Wakilai a 1999 a birnin Kano kuma ya yi nasara.
Ya nemi takarar shugabancin Majalisar inda ya yi rashin nasara ga Salisu Buhari, daga bisani ya samu goyon bayan Majalisar don zama kakakinta bayan Buhari ya bar kujerar saboda zarge-zarge.
A shekarar 2023 ya sake neman kujerar a PDP amma bai yi nasara ba saboda zargin wasu kulle-kulle da aka yi masa a siyasa.
5. Lambobin yabo
Marigayin ya samu lambobin yabo da dama daga kungiyoyi da na dalibai da gwamnati da kuma kamfanoni.
Daga cikinsu akwai lambar yabo ta CFR da tsohon shugaban kasa Jonathan ya ba shi da kuma kyautar da kungiyoyin daliban Jami'o'in BUK da Nsukka suka ba shi.
Har ila yau, kungiyar NUJ ta karrama shi da kyauta a matsayin wanda ya daga martabar dimukradiyya.
Ghali Umar Na'Abba ya rasu
A wani labarin, tsohon Kakakin Majalisar Tarayya, Alhaji Ghali Umar Na'Abba ya rasu.
Marigayin ya rasu ne a wani asibiti da ke birnin Abuja ya na da shekaru 65 a duniya.
Asali: Legit.ng