Abubuwa 28 da Ya Kamata Ku Sani Game da Marigayi Gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu
- Allah ya yi wa gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu rasuwa a Legas, bayan fama da rashin lafiya
- An sanar da rasuwar Akeredolu a ranar 27 ga watan Disamba 2023, kuma an ce ya mutu ne sakamakon cutar sankarar bargo (leukemia)
- Legit ta tattaro wasu abubuwa 28 da ya kamata ku sani game da marigayi Oluwarotimi Akeredolu, gwamnan jihar Ondo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Ondo - Rahotanni sun bayyana cewa Allah ya yi wa gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu rasu a Legas, a ranar Laraba 27 ga watan Disamba yana da shekaru 67.
An ruwaito cewa likitocin fadar gwamnati ne suka kula da lafiyarsa har zuwa ajalinsa saboda gaza kai shi kasar waje, kamar yadda wani kwamishinan Ondo ya tabbatar da mutuwarsa.
A ranar 13 ga watan Disamba ne Akeredolu ya dauki hutu don neman lafiyarsa inda Shugaba Tinubu ya ba da umurnin mika mulkin jihar hannun mataimakin Akeredolu, Mr Aiyedatiwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ga wasu abubuwa 27 da ya kamata ku sani game da marigayi Akeredolu, kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa.
Haihuwa da karatun Ekeredolu
An haifi Oluwarotimi Odunayo Akeredolu CON SAN a ranar 21 ga Yuli, 1956, a Owo ga iyalan Reverend J. Ola Akeredolu da Lady Evangelist Grace B. Akeredolu a jihar Ondo.
Akeredolu ya fara karatunsa na firamare ne a makarantar gwamnati da ke Owo, sannan ya wuce Kwalejin Aquinas da ke Akure, Kwalejin Loyola da ke Ibadan.
Sannan ya yi makarantar sakandare mai suna Ayetoro, inda ya samu shaidar kammala sakandare.
Ya tafi Jami'ar Ife (wanda a yanzu ake kira Jami'ar Obafemi Awolowo) inda ya karanta fannin shari'a kuma ya kammala a 1977.
Lakani da inkiyar Ekeredolu
Inkiyarsa ita ce Odunayo, wanda yake nufin "Shekarar farin ciki" a cikin Yarbanci.
Yana amsa sunan “Arakunrin”, yayin da lakabin sa shine “Aketi”.
Rayuwar Ekeredolu matsayin lauya
Ya kasance lauyan Najeriya kuma dan siyasa. Ya karbi rantsuwar kama aiki matsayin lauya a 1978. An nada Akeredolu a matsayin babban lauyan jihar Ondo daga 1997 zuwa 1999.
Akeredolu ya kasance manajan abokin hulda a kamfanin lauyoyin Olujinmi da Akeredolu, wanda ya kafa tare da Cif Akin Olujinmi, tsohon babban lauyan gwamnati kuma ministan shari’a na Najeriya.
A 1998, ya zama babban lauyan Najeriya, kuma ya kasance shugaban majalisar lauyoyi masu ba da taimako (2005-2006).
A cikin Nuwamba 2009, ya fuskanci zarge-zargen cin hanci da rashawa lokacin da wasu shugabannin kungiyar lauyoyi ciki har da mataimakin shugaban kungiyar suka rubuta takardar koke a kansa.
Daga nan ne majalisar zartarwa ta kasa ta kungiyar lauyoyin Najeriya ta sake duba zarge-zargen da ake masa, a karshe aka yi watsi da zargin tare da wanke shi.
Tarihin siyasar Akeredolu
watan Nuwamban shekarar 2011, Akeredolu na daga cikin gungun masu neman zama dan takarar gwamnan jihar Ondo a karkashin jam'iyyar ACN a zaben 2012.
A ranar 28 ga watan Yulin 2012 ne aka zabi Akeredolu a matsayin dan takarar gwamnan jihar Ondo a karkashin jam'iyyar ACN a Akure.
Zaben nasa ya sa ya fafata da gwamna mai ci Olusegun Mimiko da Olusola Oke na jam’iyyar PDP. Akeredolu ya yi alkawarin samar da ayyuka 30,000 a cikin kwanaki 100 na farko a ofis.
Amma duk da haka alkawarin da ya yi ya sa aka mika takardun neman aiki sama da 10,000 ga ofishin yakin neman zabensa.
An baiwa Akeredolu tikitin tsayawa takarar gwamna a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben 2016.
Wa'adin mulkin Akeredolu na farko da na biyu
A ranar Lahadi, 27 ga watan Nuwamba, 2016, ya lashe zaben fidda gwani na gwamnan jihar Ondo na 2016.
A ranar Lahadi, 27 ga Nuwamba, 2016, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta bayyana Akeredolu a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Ondo.
Ya samu kuri’u 244,842 a zaben inda ya doke Eyitayo Jegede da kuri’u 150,380 da Olusola Oke da kuri’u 126,889.
An rantsar da shi a matsayin gwamnan jihar Ondo a ranar 24 ga watan Fabrairun 2017 a Akure, babban birnin jihar Ondo.
A ranar 21 ga Yuli, 2020, an ayyana shi a matsayin dan takarar gwamnan Ondo bayan zaben fidda gwani na jam’iyyar APC, a karo na biyu.
An gudanar da zaben gwamnan jihar Ondo na 2020 a ranar 10 ga Oktoba 2020.
Akeredolu ya sake lashe zabe a karo na biyu, inda ya doke PDP Eyitayo Jegede, ZLP Agboola Ajayi, da wasu ‘yan takarar kananan jam’iyya.
Akeredolu ya rasu a ranar Laraba, 27 ga watan Disamba 2023 a jihar Legas. An ce ya mutu ne sakamakon cutar sankarar bargo (leukemia).
Gwamna Akeredolu ya riga mu gidan gaskiya
A safiyar yau ne muka ruwaito maku rasuwar gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, bayan shan fama da rashin lafiya.
Rahoton Vanguard ya ce Marigayin ya mutu ne a hannun likitocin gwamnati da ke Legas a safiyar ranar Laraba.
Asali: Legit.ng