Innaillahi: Mutane Sama da 15 Sun Mutu Yayin da Wani Abu Ya Fashe Ba Zato Ba Tsammani a Jihar PDP

Innaillahi: Mutane Sama da 15 Sun Mutu Yayin da Wani Abu Ya Fashe Ba Zato Ba Tsammani a Jihar PDP

  • Aƙalla mutane 20 suka mutu yayin wani bututun mai ya fashe a jihar Ribas ranar Lahadin da ta gabata
  • Rahotanni sun bayyana cewa ibtila'in ya afku ne yayin da wasu matasa suka fasa wani bututun, suna satar ɗanyen mai a Omoku
  • Shugaban matasan yankin ya buƙaci jami'an tsaro su kara zage damtse domin magance abubuwan da ke faruwa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Rivers - Akalla mutanen da ba su gaza 20 ba ake fargabar sun mutu biyo bayan wata fashewa da aka samu a bututun ɗanyen mai a jihar Ribas.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa fashewar bututun man ta auku ne a Omoku, ƙaramar hukumar Ogba/Egebema/Ndoni ranar Lahadi da safiya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu zata ƙwace wasu bankuna a Najeriya ta kwashe kuɗin Mutane? Gaskiya ta bayyana

Bututu ya fashe a Ribas.
Innaillahi: Mutane Sama da 15 Sun Mutu Yayin da Wani Abu Ya Fashe Ba Zato Ba Tsammani a Jihar PDP Hoto: dailytrust
Asali: UGC

An tattaro cewa lamarin ya afku ne bayan wasu matasa sun fasa bututun mai ɗaya na wani kamfanin ƙasa da ƙasa da ke aiki a yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun nuna cewa matasan na tsaka da kwasar mai da jarkoki, kwatsam abun ya fashe, ya kashe wasu yayin da wasu dama ke kwance suna karɓan magani a asibiti.

Wata majiya daga yankin ta ce:

“Wannan lamari ne mai matukar muni, mutuwar mutane 20 a irin wannan lokacin, muna zargin wasu matasa ne suka fasa bututun mai na wani kamfani."
"Idan kaje babban asibitin Omku da wasu asibitocin kuɗi na garin zaka ga mutanen da suka ji raunuka kwance suna ƙarban magani."

Yadda satar mai ya yi ajalin mutane

Shugaban kungiyar matasan Neja-Delta reshen Onelga, Emeka Ukwuosah, ya shawarci matasan yankin da su rungumi kasuwanci na halak, su guje wa sace-sacen mai.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun halaka bayin Allah sama da 100 a jihar arewa, sun tafka mummunar ɓarna

A kalamansa ya ce:

"Bari na bi sahun yin tir da sace-sacen ɗanyen mai a kewayen Onelga, sannan muna kira ga jami'an tsaro su ƙara zage dantse wajen ayyukansu a yankin."

Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Grace Iringe-Koko, ta yi alkawarin binciko abin da ya faru a fashewar kana ta waiwayi ƴan jarida.

Amma har kawo yanzu da muke haɗa wannan rahoton ba ta fitar da sanarwa a hukumance kan wannan lamari ba, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Gwamnan APC ya riga mu gidan gaskiya

A wani rahoton na daban kuma mun samu labarin cewa Allah ya yi wa gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, rasuwa.

Wasu rahotannin sun ce ‘dan siyasar ya cika ne yayin da ake kokarin kai kayan aiki domin duba shi a garin Legas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262