Mummunan Hatsarin Mota Ya Ritsa da Gomman Mutane, An Samu Asarar Rayuka

Mummunan Hatsarin Mota Ya Ritsa da Gomman Mutane, An Samu Asarar Rayuka

  • Rayukan mutum huɗu sun salwanta bayan motar da suke ciki ta gamu da mummunan hatsari a kan titin hanyar Abuja zuwa Kaduna
  • Hatsarin motan dai ya ritsa da mutum 73 da ke cikin babbar motar ɗaukar kayayyaki, inda mutum 59 suka jikkata
  • Kwamandan shiyya na hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa na jihar Kaduna ya tabbatar da aukuwar hatsarin inda ya ce an kai waɗanda suka jikkata zuwa asibiti

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa reshen jihar Kaduna ta ce mutum huɗu sun mutu yayin da wasu 56 suka samu raunuka a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Kwamandan sashin, Mista Kabir Nadabo, ya bayyana cewa hatsarin motan ya auku ne a ƙauyen Sabon Sara da ke kan babbar hanyar a ranar Talata, cewar rahotoon Daily Trust.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun halaka bayin Allah sama da 100 a jihar arewa, sun tafka mummunar ɓarna

Mutum hudu sun rasu a hatsarin mota a Kaduna
An samu asarar rayukan mutum hudu a hatsarin mota kan titin Abuja-Kaduna Hoto: FRSC Nigeria
Asali: Twitter

Nadabo ya ce hatsarin ya ritsa ne da wata tirela (Iveco) mai lamba MKA 99YS kuma ya auku ne da misalin ƙarfe 03:30 na rana, rahoton The Punch ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Tawagar ceto na rukunin RS1.113 Zhipe da RS1.17 Birnin Yero sun gudanar da aikin ceto." A cewarsa.

Menene ya haddasa hatsarin?

A cewarsa, binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa musabbabin hatsarin shi ne cunkoson kayayyaki da mutane da kuma gajiya.

"Binciken da aka yi a kan lamarin ya nuna cewa mutum 73 ne hatsarin ya ritsa da su, mutum 59 kuma sun samu raunuka, kuma abin baƙin ciki, mutum huɗu sun rasu." A cewarsa.

Ya ce an kai wadanda suka jikkata zuwa asibitocin St. Gerard da AP Smart, duk a garin Kakuri.

Nadabo ya bayyana cewa, hukumar ta FRSC za ta ci gaba da yin kira ga jama’a masu tuka ababen hawa da su bi duk ƙa’idojin hanya yayin da suke tuƙi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe ƴan kasuwa takwas, sun tafka mummunar ɓarna a jihar arewa

Mutum 11 Sun Rasu a Hatsarin Mota

A wani labarin kuma, kun ji cewa mutum 11 sun rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a jihar Jigawa.

Hatsarin motan ya auku ne bayan wasu motoci biyu sun yi taho mu gama inda dukkanin fasinjojin cikin motocin suka mutu nan take.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng