Yadda Yan Bindiga Suka Farmaki Kauyuka 23 Tare da Kashe Mutum 145 a Jihar Arewa
- Tsagerun yan bindiga sun kai kazaman hare-hare a kauyuka 23 na jihar Filato inda suka halaka mutum 145
- Maharan sun farma al'umman yankunan ne tun daga daren Asabar, 23 ga watan Disamba har zuwa wayewar garin Litinin
- A karamar hukumar Bokkos kawai sun halaka mutum 113 inda aka sheke wasu 32 a karamar hukumar Barkin Ladi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Plateau - Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa yan bindiga sun halaka akalla mutum 145 a hare-hare da suka kai kan kauyuka 23 a jihar Filato.
An rahoto cewa makasan sun murkushe mutum 113 a kauyuka 20 a karamar hukumar Bokkos da wasu 32 a kauyuka uku da ke karamar hukumar Barkin Ladi.
An tattaro cewa an farmaki kayukan ne daga daren ranar Asabar zuwa safiyar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har ila yau, an rahoto cewa hare-haren ya kuma jikkata daruruwan mutane da lalata kayayyaki.
Lamarin ya shafi kauyukan Ruku, Hurum, Darwat, Mai Yanga Sabo da NYV a yankunan Gashish da Ropp.
Shugaban karamar hukumar Bokkos ya magantu
Shugaban kwamitin rikon kwarya na karamar hukumar Bokkos, Monday Kassah, ya tabbatarwa manema labarai faruwar lamarin a jiya.
Da aka tuntube shi don ji ta bakin sa, kakakin yan sandan jihar, Alabo Alfred, bai amsa sakon waya da aka tura masa ba.
Sai dai kuma, Kyaftin Oya James, kakakin Operation Safe Haven, da ke tabbatar da zaman lafiya a jihar, ya tabbatarwa jaridar Daily Trust da faruwar lamarin.
Sai dai kuma, bai tabbatar da adadin mutanen da aka kashe ba a yanzu, amma dai ya ce an daidaita lamarin, rahoton Trust Radio.
James ya ce:
“A yanzu, an shawo kan lamarin. An tura karin tsaro zuwa yankunan da abin ya shafa. Amma ba ni da adadin wadanda suka mutu a halin yanzu."
Wani ma'aikacin jin kai da ya yi magana da sharadin sakaya sunansa ya ce sun kirga gawarwaki sama da 180 daga hare-haren.
Yan bindiga sun sace dan siyasa
A wani labarin, mun ji cewa tsagerun yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da tsohon ciyaman na karamar hukumar Yorro, Hon. Ishaya Dimas Dila, tare da wasu mutum 10 a kauyen Dila da Kunini, a ranar Lahadi.
An tattaro cewa maharan sun sace tsohon ciyaman din da wasu mutum biyu a kauyen Dila da ke karamar hukumar Yorro ta jihar Taraba a safiyar ranar Lahadi.
Asali: Legit.ng