'Yan bindiga sun halaka bayin Allah sama da 100 a jihar arewa, sun tafka mummunar ɓarna

'Yan bindiga sun halaka bayin Allah sama da 100 a jihar arewa, sun tafka mummunar ɓarna

  • Adadin mutanen da suka mutu a hare-haren da ƴan bindiga suka kai kananan hukumomi 2 a Filato ya haura 100
  • Ciyaman ɗin riƙon karamar hukumar Bokkos, Monday Kassah, ya ce zuwa yanzu sun gano gawarwaki 113 tare da masu rauni 300
  • A ranar Asabar da daddare yan bindiga sun shiga kauyuka akalla 20 a yankin, suka tafka mummunar ɓarna

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Plateau - Alamu sun nuna cewa adadin wadanda suka mutu a hare-haren da yan bindiga suka kai wasu ƙauyuka a kananan hukumomin Bokkos da Barkin-Ladi na jihar Filato sun kai 113.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa a ƙarshen makon nan da ya wuce, yan bindiga sun kashe akalla mutane 16 a kauyen Mushu da ke ƙaramar hukumar Bokkos.

Kara karanta wannan

Yadda yan bindiga suka farmaki kauyuka 23 tare da kashe mutum 145 a jihar Arewa

Yan bindiga sun halaka sama da mutum 100 a Filato.
Yan bindiga sun hakala mutane sama da 100 a kananan hukumomi 2 a Filato Hoto: Celeb Mutfwang
Asali: Facebook

Kakakin rundunar sojin Operation Save Haven, Kaftin James Oya, ya tabbatar da lamarin, yana mai cewa ƴan ta'addan sun kai mummunan harin da daren ranar Asabar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutanen da suka mutu sun haura 100

Sai dai bayanan da aka tattara ranar Litinin, 25 ga watan Disamba, 2023 sun nuna cewa adadin mutanen da suka mutu sun kai 113, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kantoman ƙaramar hukumar Bokkos a jihar Filato, Monday Kassah, ya tabbatar da cewa kawo yanzu mutane 113 ne suka mutu a hare-haren da aka kai ƙauyukan yankin.

Yayin da yake bayani kan lamarin a ranar Litinin, ya faɗa wa manema labarai cewa an tsinci gawarwaki 113 daga hare-haren da aka kai tsakanin daren Asabar zuwa safiyar Litinin.

A kalamansa ya ce:

"Ƴan bindigan sun kai hare-haren cikin tsari da shiri, kusan garuruwa 20 ne harin ƴan ta'addan ya shafa. A yanzu da nake magana da ku, mun gano gawarwakin mutum 113 daga kauyukan."

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi awon gaba da tsohon ciyaman da wasu 10 a jihar arewa

"Mun tattara mutane 300 da suka ji raunuka, wasu an kai su asibiti a Jos, wasu kuma mun kai su asibitin Barkin Ladi yayin da wasu aka kwantar da su a asibitin Bokkos."
"Jami'an tsaro suna iya bakin ƙoƙarinsu, rashin kyaun hanya zuwa kauyukan ne ya kawo cikas ga jami'an tsari ba su iya zuwa suka dakile munanan hare-haren ba."

'Yan Bindiga Sun Kashe Yan Kasuwa Takwas a Katsina

A wani rahoton na daban 'Yan bindiga sun halaka ƴan kasuwa takwas da ke kan hanyar dawowa daga kasuwar mako-mako a Jibia, jihar Katsina.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun buɗe wa motar da yan kasuwan ke ciki wuta, suka raunata wasu mutum huɗu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262