"Ba Sabiu Tunde Yusuf Bane", Emefiele Ya Bayyana Wanda Ya Bada Umurnin Sauya Fasalin Naira
FCT Abuja - Tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, a ranar Lahadi, 24 ga watan Disamba, ya ce tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne ya bada umurnin sauya fasalin naira.
Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe
Kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto, Emefiele ya bayyana hakan ne kan rahoton mai bincike kan harkokin CBN, Jim Obazee, wanda ya yi ikirarin cewa shugaban kasa bai bada amincewarsa ba kafin yin sauyin fasalin nairan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Emefiele ya ce mafi yawancin abin da aka ce rahoton ya kunsa da ake rahotowa a kafafen watsa labarai ba gaskiya bane, kuma ana hakan ne don bata masa suna, cin mutuncinsa da kuma wata manufa ta sonkai na mai binciken, Business Day ta rahoto.
Wani sashi na tsokacin Emefiele ta ce:
Dakaci karin bayani ...
Asali: Legit.ng