Rundunar Yan Sanda Ta Yi Martani Bayan Dan Sanda Ya Bindige Jarumin Fim, Ta Fadi Matakin Dauka
- Rundunar ƴan sandan jihar Ogun ta fitar da sanarwa dangane da harbin da aka yi wa jarumin fina-finan Nollywood, Azeez Ijaduade
- Kamar yadda rahotanni suka nuna wani jami’in ƴan sanda ne ya harbi jarumin a ranar Asabar 23 ga watan Disamba, 2023
- Biyo bayan harbin da ake zargin dan sandan ya yi, yanzu haka daraktan fim kuma furodusan Ijaduade yana samun kulawar likitoci
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Ogun - Rundunar ƴan sandan jihar Ogun ta tofa albarkacin bakinta dangane da harbin da aka yi wa fitaccen ɗan wasan Nollywood Azeez Ijaduade a gundumar Iperu ta jihar.
Rahotanni sun bayyana cewa, Ijaduade, daraktan fina-finai kuma furodusa, a halin yanzu yana karbar magani a asibitin koyarwa na jami’ar Babcock da ke jihar Ogun sakamakon harbin da ake zargin wani ɗan sanda ya yi masa.
A daren Asabar, abokin aikin Ijaduade, Abiodun Adebanjo, ya bayyana lamarin a shafin sa na Instagram.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me rundunar ƴan sandan ta ce dangane da harbin?
Jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar ƴan sandan jihar Ogun, SP Omolola Odutola, ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa a ranar Lahadi, inda ta ce harsashi ne ya raunata jarumin bayan wani ɗan sanda da ke aiki da wani ɗan ƙasar China ya harbi iska.
Odutola ta bayyana cewa Ijaduade na samun sauƙi, kuma an gano jami’in ɗan sandan, inda har an fara gudanar da bincike kan lamarin.
Matashiya ta kashe abokin mijinta
A baya labari ya zo cewa wata matashiya matar aure ta yi sanadiyyar salwantar da ran abokin mijinta a jihar Kano.
Rundunar ƴan sandan jihar ta cafke matashiyar wacce ake zargin sun haɗa kai da mijinta wajen halaka abokin nasa.
Ƴan Sanda Ta Cafke Tubabben Ɗan Fashi da Makami
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Kano ta sake kama wani ƙasurgumin ɗan fashi wanda ya tuba kwanaki, Bahago Afa, tare da wasu ƴan fashi shida.
Rundunar ta ƙara da cewa, jami’anta sun yi nasarar dakile wasu hanyoyin sadarwa na masu aikata laifuka da suka mayar da jihar ta zama cibiyar daba, fashi da makami, da sauran miyagun ayyuka.
Asali: Legit.ng