Gwamnatin Tinubu Za Ta Kwace Bankuna 2 da Aka Siyar a Lokacin Emefiele, An Bayyana Dalili
- Gwamnatin Najeriya za ta duba yiwuwar karɓe wasu bankuna biyu da aka sayar a zamanin Godwin Emefiele a matsayin gwamnan CBN
- Matakin ya biyo bayan bayanan da wani mai bincike na musamman ya bayar cewa an sayar da bankunan ba tare da shaidar biyansu ba
- Akwai kuma zargin cewa ɗaya daga cikin masu zuba hannun jarin bankunan ya yi karya lokacin siyan bankin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - An buƙaci gwamnatin tarayya da ta ƙwace wasu bankunan Najeriya guda biyu da aka sayar a zamanin Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN).
Bankunan sun haɗa da Union Bank of Nigeria da Keystone Bank.
Matakin dai na zuwa ne bayan shafe kusan watanni shida ana gudanar da bincike kan ayyukan CBN a ƙarkashin Emefiele da wani mai bincike na musamman, Jim Obazee, wanda Shugaba Bola Tinubu ya naɗa, inda ya yi zargin an tafka cin hanci da rashawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar rahoton da aka miƙa wa shugaban ƙasar, ya bayyana cewa an sayar da bankunan biyu ba tare da bin ƙa’ida ba.
Domin haka, mai binciken ya ba da shawarar cewa gwamnatin tarayya ta ƙwace bankunan biyu tare da mayar da su na ƙasa.
Siyar da bankin Union
A cewar mai binciken, yayin da aka ce masu hannun jarin Union Bank na zaune a ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa, binciken gaskiya ya nuna cewa ba su a Dubai.
Wani ɓangare na rahoton na cewa:
"A lokacin da muka gudanar da bincike, mun gano cewa Mista Godwin Emefiele ne ya yi amfani da wasu mutane a matsayin wakili suka kafa bankin Titan Trust kuma suka siya Union Bank daga nan. Duk daga dukiyar da ba ta dace ba."
"An gano cewa waɗannan mutanen ba su a Dubai kamar yadda suka yi iƙirari."
"Wannan ya ci karo da sashe na 3 (5) na dokar Bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kuɗi na shekarar 2020. Domin haka bai kamata a bar su su yi aiki ko su mallaki banki a Najeriya ba."
Siyar da bankin Keystone
Mai binciken ya kuma bayyana yadda aka siya bankin "Keystone kyauta."
A cewar rahoton, duk da cewa an siyar da Keystone gaba ɗaya, babu wata shaida ta biyan kudin siyan bankin.
Wani ɓangare na rahoton yana cewa:
"An yi amfani da wasu mutane a matsayin wakilai tare da haɗin kai da taimakon Mista Godwin Emefiele da kuma CBN wajen siyan bankunan biyu.
"Lokacin da muka gudanar da bincike, mun gano cewa an yi amfani da wasu mutane a matsayin ƴan amshin shata tare da haɗin kai da taimakon Mista Godwin Emefiele da kuma CBN wajen mallakar bankin Keystone ba tare da shaidar biyan kuɗi ba."
An Bayar da Belin Emefiele
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya fita daga gidan gyaran hali na Kuje.
Emefiele ya bar gidan gyaran halin ne bayan ya cika sharuɗɗan belin da alƙalin babbar kotun tarayya da ke Abuja, ya gindaya masa.
Asali: Legit.ng