Ana Cikin Bankado Sababbbin Laifukan Emefiele, Kotu Ta Bayar da Sabon Umarni Kan Tsohon Gwamnan CBN
- Bayan kwashe lokaci mai tsawo a gidan gyaran hali na Kuje da ke babban birnin tarayya Abuja, an bayar da belin Emefiele
- Tsohon gwamnan na babban bankin Najeriya (CBN) ya bar gidan gyaran hali na Kuje ne bayan ya cika sharuɗɗan belinsa
- Alƙalin babbar kotun tarayya da ke babban birnin tarayya Abuja ya bayar da belin Emefiele kan kuɗi N300m tare da kawo mutum biyu da za su tsaya masa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele ya cika sharuɗɗan belin da mai shari’a Hamza Mu’azu na babbar kotun babban birnin tarayya Abuja, dake Maitama ya bayar.
Mai shari’a Mu’azu ya bayar da belin Mista Emefiele a kan kuɗi Naira miliyan 300.
An kuma buƙaci ya gabatar da mutum biyu da za su tsaya masa, waɗanda suka mallaki kadara a gundumar Maitama da ke babban birnin tarayya Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tattaro cewa sanarwar sakin Emefiele na dauke da sa hannun alƙali mai shari'a Othman Musa, a ranar 22 ga watan Disamba.
Yaushe aka saki Emefiele?
Kakakin gidan gyaran hali na Kuje, babban birnin tarayya Abuja, Adamu Duza, ya tabbatar wa da jaridar The Punch faruwar lamarin a ranar Asabar.
"Zan iya tabbatar muku da cewa shi (Emefiele) ya cika sharuɗɗan belinsa, domin haka ba shi da dalilin cigaba da zama a gidan gyaran hali" A cewarsa.
"Ya cika sharuɗɗan belinsa kuma an sake shi da misalin karfe 2:00 na rana a jiya (Juma'a)."
An dai gurfanar da Emefiele ne a gaban kotun bisa zarge-zarge shida na yin sama da faɗi da N1.9bn.
Laifuka 20 Na Godwin Emefiele
A wani labarin kuma, kun ji cewa babban mai bincike kan babban bankin Najeriya (CBN), Jim Obaze, ya gabatar da rahotonsa kan binciken da ya gudanar.
Obaze a cikin rahoton da ya gabatarwa Shugaba Tinubu, ya zayyano manyan laifuka 20 da ake tuhumar tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele da aikatawa.
Asali: Legit.ng