Tsohon Shugaban APC Ya Faɗi Mataki 1 da Buhari Ya Ƙi Ɗauka Wanda Ya Jefa Yan Najeriya a Wahala
- Bisi Akande, tsohon shugaban APC na rikon kwarya ya ce Muhammadu Buhari ya kamata a ace ya cire tallafi tun farko
- Akande, tsohon gwamanan jihar Osun ya ce da an cire tallafin a lokacin Buhari da yan Najeriya ba zasu wahala a lokacin Tinubu ba
- Ya bayyana yadda suka tsara cire tallafin tun kafin rantsar da Buhari amma lamarin ya ci tura bayan hawa mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
FCT Abuja - Tsohon gwamnan jihar Osun, Adebisi Akande, ya bayyana cewa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya samu damar cire tallafin man fetur a lokacin mulkinsa.
Akande ya bayyana cewa da tun lokacin Buhari ya cire tallafin da zuwa yanzun ƴan Najeriya sun saba da wahalar da zata biyo baya.
Tsohon gwamnan ya yi wannan furucin ne yayin hira da Channels tv a sabon shirin da suka fara gudanarwa mai suna, "Inside Sources."
Akande, wanda yana cikin gwamnati a wancan lokacin, ya nuna rashin jin dadinsa game da matakin da gwamnatin Buhari ta dauka na tattalin arziki tun daga farko.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Duk da ya nuna damuwarsa, Akande ya ce ba zai fito ya soki Gwamnatin Muhammadu Buhari ba, yana mai nuni da matsayinsa a lokacin.
Yadda muka yi da Buhari tun a zangon farko - Akande
Akande, tsohon shugaban jam'iyyar APC na rikon kwarya, ya ce:
"Daga lokacin da Buhari ya lashe zaben shugaban ƙasa zuwa lokacin da aka rantsar da shi, mun yi tattaunawa da taruka da dama domin a cire tallafin man fetur."
"Bayan rantsar da shi, ya fara taka tsantsan, yana tafiyar hawainiya har zangon farko ya kare. Ya so ya cire tallafin, amma kasa ta ɗauki zafi kan batun, sai ya ja da baya."
"Tun farko ban gamsu da Buhari ya ci gaba da biyan tallafin ba. Ya kamata a cire tallafin mai a lokacinsa, da a yanzu ‘yan Nijeriya sun saba da shi kuma da ya yi laushi."
A cewar tsohon gwamnan, ya yi hasashen cewa shawarwari masu kyau da aka bai wa Buhari ne suka yi tasiri wajen tafiyar da harkokin biyan tallafin, cewar The Cable.
TUC ta yi barazanar shiga yajin aiki
A wani rahoton kuma Kungiyar TUC ta yi barazanar shiga yajin aiki matuƙar CBN bai gaggauta magance ƙarancin takardun Naira ba
A wata sanarwa da ƙungiyar kwadagon ta fitar ranar Jumu'a, ta ce ƴan Najeriya na cikin ƙunci sakamakon rashin kuɗi a hannu
Asali: Legit.ng