Ana Dab da Kirsimeti Shugaba Tinubu Ya Aike da Sako Mai Ratsa Zuciya Ga Yan Najeriya
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyaana cewa zai yi adalci ga kowa ba tare da la'akari da bambancin ƙabila ko addini ba
- Shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a birnin Legas bayan ya yi Sallar Juma'a a masallacin ƙungiyar Ansar-Ud-Deen
- Tinubu ya yi nuni da cewa yana sane da halin da ake ciki kuma gwamntinsa na aiki tuƙuru domin ragewa ƴan Najeriya raɗaɗi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar da cewa zai kasance mai adalci a koyaushe ga ƴan Najeriya, kuma gwamnatinsa ta jajirce wajen ciyar da haɗin kan Nijeriya gaba da tabbatar da walwala da wadata ga ƴan kasa baki ɗaya.
Ya yi wannan alƙawarin ne a babban masallacin Ansar-Ud-Deen da ke Surulere, Legas, a ranar Juma’a, 22 ga watan Disamban 2023.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arziƙi da gwamnatinsa ta ɓullo da su na da nufin samar da tsayayyen tushe mai inganci ga ƴan Nijeriya na yau da masu zuwa nan gaba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar wata sanarwa da Ajuri Ngelale, ya fitar, Tinubu ya gudanar da Sallar Juma'a a masallacin ƙungiyar Ansar-Ud-Deen Society of Nigeria (ADS) inda ya yaba da gudunmawar da suke bayarwa ga addinin Musulunci, da tallafawa marasa ƙarfi.
Ya kuma yi kira ga mambobin da su ci gaba da jajircewa kan manufofinsu na ciyar da ilimin ƴan ƙasa gaba, tare da bunƙasa kyawawan halaye da zamantakewar al’ummar musulmi.
'Sauki na nan tafe' - Tunibu
Da yake nanata ƙudurinsa na kyautata rayuwar ɗaukacin ƴan ƙasa, Shugaba Tinubu, wanda yake takaitaccen hutun Kirsimeti a Legas, ya ce an rage kashi 50 cikin 100 na kuɗin zirga-zirga a tsakanin jihohi a faɗin ƙasar nan, da kuma biyan kuɗaɗen alawus-alawus na masu cin gajiyar N-Power.
Ya ce ya yi hakan ne domin duk kokarin da ake yi na rage radadin da ƴan Najeriya ke fama da su a wannan kakar bukukuwan, inda ake sa ran kawo sababbi a sabuwar shekara.
Ya ƙara da cewa:
“Mun himmatu wajen tabbatar da yanayi mafi inganci ga ƴan ƙasa ba tare da la’akari da bambancin ƙabila, addini ko yanki ba. Manufofi daban-daban da aka riga aka aiwatar ana sa ran za su kawo babban taimako ga mutanenmu. Mun san ciwon su, kuma muna magance su gaba ɗaya."
Gwamnati Za Ta Saki Sunayen Waɗanda Za a Ba Tallafi
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta yi alƙawarin bayyana sunayen mutanen da za su amfana da tallafin N50,000.
Ministar jin ƙai, Dr. Betta Edu ita ce ta yi wannan alƙwarin inda ta ce za a wallafa sunayen ne a cikin watan Janairun 2024.
Asali: Legit.ng