Yan Najeriya Na Tsaka Mai Wuya Yayin da TUC Ta Fitar da Sabuwar Sanarwa Kan Ƙarancin Naira

Yan Najeriya Na Tsaka Mai Wuya Yayin da TUC Ta Fitar da Sabuwar Sanarwa Kan Ƙarancin Naira

  • Kungiyar TUC ta yi barazanar shiga yajin aiki matuƙar CBN bai gaggauta magance ƙarancin takardun Naira ba
  • A wata sanarwa da ƙungiyar kwadagun ta fitar ranar Jumu'a, ta ce ƴan Najeriya na cikin ƙunci sakamakon rashin kuɗi a hannu
  • Ta buƙaci Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta kawo ƙarshen lamarin kafin ƴan kwadago su ɗauki zaɓinsu na karshe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Kungiyar kwadago ‘Trade Union Congress of Nigeria’ (TUC) ta bukaci babban bankin Najeriya (CBN) ya kawo karshen karancin Naira a fadin kasar nan.

TUC ta ce matsin karancin Naira ka iya tilasta mata tare da kawayenta su duba yuwuwar, "amfani da zaɓin mu na karshe a duk lokacin da aka kai ma'aikata bango."

Kara karanta wannan

Kotun Koli ta yanke hukuncin ƙarshe kan nasarar gwamnan PDP a zaben 2023

Takardun kuɗin Najeriya.
TCN Ga CBN: Ku Kawo Karshen Karancin Takardun Naira Ko Mu Shiga Yajin Aiki Hoto: CBN
Asali: UGC

Kungiyar kwadagon ta bayyana haka ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban TUC na kasa, Festus Osifo da sakatare, Nuhu Toro, ranar Jumu'a, 22 ga watan Disamba, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda mutane suka sake shiga ƙunci

Ƙungiyar ta koka kan yadda ƴan Najeriya suka shiga ƙunci da wahalar ƙarancin Naira a hannu, yayin da bankuna da ATM suka rage baiwa mutane tsabar kudi.

A cewar TUC, lamarin ya tilastawa mutane komawa amfani da masu sana'ar POS, waɗanda suke cajin mutane kuɗi yadda ransu ke so, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Sanarwan ta ce:

"Kungiyar TUC ta zuba ido tare da damuwa bisa yadda kwatsam, matsanancin karancin kudin mu na gida watau Naira ke ƙara jefa mutane cikin kunci a fadin kasar nan."
"Ƴan Najeriya sun wayi gari cikin wahalar samun kuɗi daga bankuna da ATM, wanda ya sa dole suka koma wajen masu POS da ke yadda suka ga dama wajen cajin mutane."

Kara karanta wannan

Waiwaye ga 2023: Manyan shugabannin 'yan ta'adda 5 da aka halaka a shekara mai karewa

"Muna mamakin yadda CBN ya gaza wadatar da takrdun Naira ga ma'aikata da ƴan ƙasa."

Sanarwan ta ƙara da bayanin cewa kungiyar ba zata lamurci ci gaba da jefa al'umma cikin ƙuncin rashin wadakatar Naira ba, kamar yadda Vanguard ta tattaro.

Ta kuma buƙaci gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ta gaggauta kawo ƙarshen wannan batun karancin Naira ko kuma ƴan kwadago su shiga yajin aiki.

Ana zargin Emefiele ya sayi bankuna 3

A wani labarin kun ji cewa Rahoton binciken da aka gudanar kan CBN ya nuna yadda Godwin Emefiele ya kwashi kuɗi ya mallaki bankuna har guda uku.

Jim Obazee, mai bincike na musamman da aka naɗa kan lamarin ya miƙa rahoto ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262