An Gano Yadda Tsohon Gwamnan CBN Ya Yi Amfani da Wasu Manyan Mutane Ya Siye Bankuna 3

An Gano Yadda Tsohon Gwamnan CBN Ya Yi Amfani da Wasu Manyan Mutane Ya Siye Bankuna 3

  • Rahoton binciken da aka gudanar kan CBN ya nuna yadda Godwin Emefiele ya kwashi kuɗi ya mallaki bankuna har guda uku
  • Jim Obazee, mai bincike na musamman da aka naɗa kan lamarin ya miƙa rahoto ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ranar Laraba
  • A cikin wannan rahoton, ya zargi Emefiele da amfani da wakilai wajen sayen bankin Union, Polaris da Keystone

FCT Abuja - Rahoton binciken da aka yi kan babban bankin Najeriya na ƙara bayyana yadda tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya ci karensa babu babbaka.

Wata badaƙala da aka sake bankaɗowa ta nuna cewa ana zargin Emefiele ya yi amfani da wasu mutane a matsayin wakilai wajen siyen bankin Union Bank of Nigeria (UBN).

Tsohon gwamnan CBN, Mista Godwin Emefiele.
Yadda Emefiele Ya Yi Amfani da Wasu Mutane Wajen Siyen Bankuna 3 a Mulkin Buhari Hoto: Mr Godwin Emefiele
Asali: Facebook

Wannan na ɗaya daga cikin zarge-zargen da Jim Obazee, mai bincike na musamman da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa, ya rubuta a rahotonsa.

Kara karanta wannan

Ana dab da Kirsimeti Shugaba Tinubu ya aike da sako mai ratsa zuciya ga yan Najeriya

Haka nan kuma rahoton ya gano cewa marigayi Alhali Usma'ila Funtua tare da Emefiele na da hannu wajen cefanen bankin Keystone da Bankin Polaris, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marigayi Funtua na ɗaya daga cikin na hannun daman tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, wanda rahoton ya zargi suna da hannu a sayen bankuna 2 tare da Emefiele.

Abin da rahoton binciken ya nuna

An yi ciniki tare da sayen waɗannan bankuna uku, Union, Plaris da Keystone a lokuta daban-daban kamar yadda rahoton ya nuna ɓaro-ɓaro.

A ranar Laraba, 20 ga watan Disamba, 2023, mai binciken mai zaman kansa ya miƙa rahoton abubuwan da ya gano a CBN ga Shugaba Bola Tinubu.

A ranar 30 ga Yuli, 2023 ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada Obazee, babban jami’in hukumar bayar da rahoton kudi ta Najeriya a matsayin mai bincike na musamman.

Kara karanta wannan

Boye N600bn da abubuwa 20 da binciken Tinubu ya tono a ‘badakalar’ Emefiele a CBN

The Nation ta ruwaito cewa mai binciken ya rubuta a rahotonsa cewa:

“Lokacin da muke gudanar da binciken mu, mun gano cewa Mista Godwin Emefiele ne ya yi amfani da wasu mutane wajen kafa bankin Titan Trust da kuma mallakar bankin Union, duk daga dukiyar haram."
"Mun samu nasarar gano wasu muhimman takardu kuma wannan rahoton bincike ka iya baiwa gwamnatin tarayya damar kwace bankunan guda biyu."

Babu izinin Buhari a sauya takardun Naira

A wani rahoton kuma an bankaɗo wanda ya bada umarni ga gwamnan CBN ya canza Naira ba tare da amincewar Muhammadu Buhari ba.

Jim Obazee, mai binciken CBN mai zaman kansa wanda Shugaba Bola Tinubu ya naɗa ne ya bayyana haka a rahotonsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262