"Na Kashe Shi Ne Saboda Ya Hana Ni Kashe Kaina": Matar da Ake Zargi da Kashe Abokin Mijinta a Kano

"Na Kashe Shi Ne Saboda Ya Hana Ni Kashe Kaina": Matar da Ake Zargi da Kashe Abokin Mijinta a Kano

  • Rundunar yan sandan jihar Kano ta gurfanar da matashiya yar shekaru 24 da ake zargi da kashe abokin mijinta
  • Wacce ake zargin, Hafsat Sirajo wacce mata ce a wajen Dayyabu Abdullahi, ta amsa laifinta yayin zantawa da manema labarai
  • Za a gurfanar da ita a gaban kotu bayan kammala bincike kan shari'ar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kano - Rundunar yan sandan jihar Kano ta gurfanar da wata matashiyar mata mai suna Hafsat Sirajo, wacce ake zargi da kashe abokin mijinta, Nafiu Hafizu.

Kwamishinan yan sandan jihar, Muhammad Usaini Gumel, ne ya gabatar da matashiyar a gaban manema labarai a ranar Juma'a, 22 ga watan Disamba.

Yan sandan Kano sun gurfanar da matar da ake zargi da kisan kai
“Na kashe shi ne saboda ya hana ni kashe kaina”: Matar da ake zargi da kashe abokin mijinta a Kano Hoto: Kano State Police Command
Asali: Facebook

Matashiyar wacce ke zaune a unguwa Uku da ke karamar hukumar Tarauni ta jihar Kano ta amsa laifin da ake zargin ta aikata.

Kara karanta wannan

Yan sandan Kano sun kama tubabben dan fashi da makami, suna neman wasu 72 ruwa a jallo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan sanda sun kama Hafsat tare da mijinta, Dayyabu Abdullahi da kuma mai gadinsu Malam Adam.

Ana tuhumarsu da taimakawa matashiyar wajen biye gawar marigayin da kokarin yi masa jana'iza ba tare da an ankara cewa kashe shi suka yi ba.

"Na caccaka masa wuka" - Hafsat

A cikin wani faifan murya da ya bayyana a soshiyal midiya an jiyo Hafsat tana cewa:

"Mun yi dabbe da shi ya kwace wukar a hannuna ne, toh na yanke a hannuna jini yana ta zuba sai ya ce in je in cire kayan jikina, na je na cire na sa wasu. Toh na fito daga bandakin sai na gan shi yana kwance, don dama ba ma shi da lafiya ya sha magani ne yana kwance, kawai sai na ga wukar a gefen shi, shine na dauka na dunga daddaba mashi yana gudu na bi shi da shi har sama, shine ya tsallaka balkoli ya kwanta ni kuma sai na sauko na fita a gidan na tafi kemis aka wanke mun."

Kara karanta wannan

Ina za ki damu: Mata ta hada baki da mijinta sun hallaka abokinsa a Kano

A nashi bangaren, mijin ya ce baya nan da abun ya faru sai da yamma ta kira shi a waya ta fada mai cewa sun yi fada da Nafiu har ya kai mata wuka zai yanke ta ita kuma ta kwace ta caccaka masa, saboda wannan ya rasu.

Ya kuma ce dama a baya tana yawan cewa za ta kashe kanta inda ta kan dauko makami sai ya yi da gaske ya kwace.

Ga faifan hirar tasu da manema labaran a kasa:

Legit Hausa ta tuntubi wata ta kusa Hafsat wacce ta nemi a sakaya sunanta don jin ta bakinta inda tace:

“Innalillahi wa’inna illahi raji’un. Wallahi tunda abun nan ya faru na kasa baccin kirki, na kasa gasgatawa wai Hafsat za ta iya kashe mutum. Ku dai Allah ya raba mu da mummunan kaddara amma duk wanda ya santa ya san mutuniyar kirki ce. Ina rokon Allah ya sa ta ci wannan jarrabawa. Ameen."

Kara karanta wannan

Hawaye sun kwaranya yayin da jami'in soja ya mutu a hanyarsa ta zuwa daurin aurensa

Kisan gilla suka yi masa, mahaifin Nafiu

A baya mun ji cewa mahaifin marigayi Nafiu ya yi zargin cewa kisan gilla Hafsat suka yi wa dansa a jihar Kano.

Malam Hafizu wanda ya fito daga jihar Bauchi ya ce da farko sun masa karya cewa ciwon shi ne ya tashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng