Yan Sandan Kano Sun Kama Tubabben Dan Fashi da Makami, Suna Neman wasu 72 Ruwa a Jallo
- Jami'an yan sandan jihar Kano sun kama wani kasurgumin shugaban masu fashi da makami, Bahago Afa da wasu mutum shida
- Haka kuma, rundunar yan sandan ta ayyana neman wasu masu aikata laifi 72 ruwa a jallo
- Kwamishinan yan sandan Kano, Usaini Gumel ya ce sun yi maganin Daba a Kano amma sai miyagun suka billo da wasu hanyoyi na yin fashi da makami
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Kano - Rundunar yan sandan jihar Kano ta sake kama wani kasurgumin dan fashi wanda ya tuba kwanaki, Bahago Afa, tare da wasu yan fashi shida.
Rundunar ta kara da cewa, jami’anta sun yi nasarar dakile wasu hanyoyin sadarwa na masu aikata laifuka da suka mayar da jihar ta zama cibiyar daba, fashi da makami, da sauran miyagun ayyuka, rahoton Punch.
Kwamishinan yan sandan jihar, Usaini Gumel, ya bayyana hakan yayin da yake gurfanar da madugun yan fashin da sauransu a ranar Juma'a, 22 ga watan Disamba, rahoton New Telegraph.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce:
"Dama dai, akwai tubabbun masu laifi fiye da 700 a jerinmu, kuma duk wanda ya kuskura ya koma cikinsu za a ayyana shi a matsayin makiyin zaman lafiya kamar dai Bahago Afa da sauransu."
A cewar Gumel, an sake kama wadanda ake zargin ne a mabuyarsu.
Ya kara da cewar:
"A yau, mun yi maganin Daba, amma a yau suna aiwatar da ayyukan fashi da makami, da shirya laifuka na fashi da makami.
"Gaba daya wadanda aka ayyana a matsayin makiyan zaman lafiya, ana neman 72 daga cikinsu ruwa a jallo kuma duk inda yan sanda ko wani ya gansu, a kama su sannan a kawo su gaban yan sanda."
Matashiya ta kashe abokin mijinta a Kano
A wani labari na daban, mun ji cewa wata matar aure ta shiga hannu kan zargin hada kai da mijinta inda suka kashe abokinsa.
Kamar yadda @Ussyy___ ya wallafa a shafinsa na X, wanda aka fi sani da Twitter a baya, daya daga cikin yan uwan mamacin mai suna Sunusi Abdullahi Gwarando ya tabbatar da faruwa lamarin.
Asali: Legit.ng