Shugaba Tinubu, Zulum da Wasu Manyan Ƙusoshi da Zasu Halarci Gasar Karatun Alqur'ani Mai Girma

Shugaba Tinubu, Zulum da Wasu Manyan Ƙusoshi da Zasu Halarci Gasar Karatun Alqur'ani Mai Girma

  • Bola Ahmed Tinubu na cikin manyan baƙin da ake sa ran zasu halarci gasar karatun Alkur'ani Mai Girma na ƙasa a jihar Yobe
  • Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Gwamna Zulum da takwaransa Mai Mala Buni na cikin waɗanda ake sa ran zasu halarci wurin
  • A ranar Jumu'a 29 ga watan Disamba, 2023 za a buɗe gasar karatun ta bana a Damaturu, babbak birnin jihar Yobe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Damaturu, jihar Yobe - Ana tsammanin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai halarci gasar karatun Alƙur'ani ta ƙasa da aka shirya yi a Damaturu, babban birnin jihar Yobe.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Tinubu, Gwamna Zulum da Wasu Jiga-Jigai Zasu Halarci Gasar Alkur'ani Ta Kasa a Yobe Hoto: @NGRPresident
Asali: Facebook

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar na III, gwamnonin jihohin Borno da Yobe, Babagana Zulum da Mala Buni, na cikin waɗanda ake sa ran zasu halarci wurin.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Zanga-zanga ta ɓarke a gidan gwamnatin jihar PDP kan muhimmin batu

Kwamishinan ma'aikatan cikin gida, yaɗa labarai da al'adu na jihar Yobe, Abdullahi Bego, shi ne ya faɗi haka yayin hira da ƴan jarida a sakateriyar NUJ da ke Damaturu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manyan mutanen da zasu halarci wurin

Ya ce gasar karatun Alkur'anin da za a fara ranar Juma’a 29 ga watan Disamba zai samu shugaba Tinubu a matsayin babban bako na musamman, cewar Daily Trust.

Haka nan kuma gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum zai shugabanci bikin rufewa.

Sai kuma Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar wanda ake ran zai halarci wurin a matsayin uban ƙasa.

Yayin da ministan harkokin ƴan sanda, Sanata Ibrahim Geidam, zai kasance shugaban bikin buɗe gasar karatun na littafi mai tsarki.

A cewar Bego, kimanin mutane 296 da za su fito daga jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja ne zasu fafata a gasar mai kunshe rukunoni 10.

Kara karanta wannan

Karshen shekara: Manyan malaman addinin musulunci 5 da suka rasu a 2023

Ya ce Yobe na da mutane takwas da zasu shiga gasar kuma bisa irin goyon baya da horon da suka samu, jihar na da kwarin gwiwar cewa za su yi nasara a gasar.

Gwamnatin Tinubu Ta Fitar da Sanarwa Kan Biyan Kuɗin N-Power

A wani rahoton na daban Gwamnatin Najeriya ta fara yi wa masu cin gajiyar tsarin Npower ruwan alert na kuɗaɗen da suke bin bashi.

Ministar jin kai da yaƙi da talauci, Dokta Betta Eddu, ta tabbatar wa ƴan Npower cewa kowa zai ga kuɗinsa a asusun banki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262