Bidiyo Ya Bayyana Yayin da Alkaliyar Kotun Koli Ta Kira Sanatoci da Mijinta Yayin Tantance Ta
- Mai shari'a Jummai Sankey Jo, wacce aka zaba don shiga Kotun Koli, ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya
- Ta ja hankali sosai a soshiyal midiya lokacin da ta kira sanatoci a matsayin mijinta yayin tantance ta a zauren majalisar dattawan
- Yayin da mutane da dama suka caccaketa kan yin wannan furuci don samun shiga, wasu sun bayyana hakan a matsayin mutunta al'ada
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
FCT, Abuja - Yayin tantance ta a zauren majalisar dattawa don hawa mukamin Alkaliya ta Kotun Koli, Jummai Sankey Jo, Mai shari'a ta Kotun Daukaka Kara, reshen Owerri, ta kira sanatocin jihar Kaduna da "mazajenta".
Ta yi wannan jawabin ne yayin da ta bayyana a gaban yan majalisa a ranar Laraba, 20 ga watan Disamba sannan aka daura bidiyon a dandalin X, wanda aka fi sani da Twitter a baya.
Ta ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Na fito daga jihar Filato. Na lura cewa bani da wani wakili da ke mara mun baya a nan. Amma, jihata ta aure ita ce jihar Kaduna."
Sankey, daya daga cikin alkalai 11 da aka zaba, ta nuna damuwa game da rashin kasancewar kowani dan majalisa daga mahaifarta ta jihar Filato cikin mambobin kwamitin.
Sai dai kuma, ta samu nutsuwa a gaban wani sanata daga jihar Kaduna, tana mai tabbatar da cewar mijinta dan Kaduna ne, kuma saboda haka, tana daukar yan majalisar na Kaduna a matsayin mazajenta.
Jama'a sun yi martani kan bidiyon
@Jonehmk ya rubuta:
"Toh ta yaya za ki yi hukunci cikin adalci idan daya daga cikin mazajenki ya dulmiya hannayensa a baitun malin al'umma?"
@niyiogunkoya ya rubuta:
"Kalli alkaliya tana zawarcin sanatoci a Najeriya. Wannan mace ce da shakka babu tana da digiri na biyu a bangaren shari'a, sannan ga ta tana zawarcikin (wasu) masu takardar firamare. Ina nufin kamar @MBuhari. Duk kun ji kunya."
@victorumesi, da yake kare alkaliyar ya ce:
"Tana magana ne musamman kan sanata mai ci da manyansa daga karamar hukuma daya da mijinta a jihar Kaduna."
@Hola_Bishop ya rubuta:
"Kiran sanata daga yankinta. Al'adar Afrika. Ana daukar surukai a matsayin miji. Babu wata matsala a nan."
Majalisa ta amince da alkalan Kotun Koli 11
A gefe guda, mun jin cewa majalisar dattawan Najeriya ta amince da naɗin sabbin alƙalai 11 a kotun koli waɗanda shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya aiko mata da sunayen su.
Tinubu ya buƙaci majalisar ta amince da alƙalai 11 domin su cike guraben da suka rage a kotun koli mai daraja ta ɗaya a ƙasar nan, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Asali: Legit.ng