Majalisar dattawa Ta Amince da Buƙatar Tinubu a Kotun Ƙoli Ana Shirin Yanke Hukunci Kan Zaben Kano

Majalisar dattawa Ta Amince da Buƙatar Tinubu a Kotun Ƙoli Ana Shirin Yanke Hukunci Kan Zaben Kano

  • Majalisar dattawa ta tabbatar da naɗin alƙalai 11 da zasu cike wasu gurabe da ake da su a kotun kolin Najeriya
  • A zaman ranar Alhamis, 21 ga watan Disamba, 2023, majalisar ta amince da naɗin bayan karɓan rahoto daga kwamitin shari'a
  • Jiya Laraba, Bola Ahmed Tinubu ya miƙa sunayen alkalan ga majalisar dattawan bayan shawarin hukumar shari'a ta ƙasa NJC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Majalisar dattawan Najeriya ta amince da naɗin sabbin alƙalai 11 a kotun koli waɗanda shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya aiko mata da sunayen su.

Tinubu ya buƙaci majalisar ta amince da alƙalai 11 domin su cike guraben da suka rage a kotun koli mai daraja ta ɗaya a ƙasar nan, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Labari mai daɗi: Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan ƙarancin takardun Naira, ta nemi afuwa

Kotun kolin Najeriya.
Majalisar dattawa ta amince da buƙatar Tinubu a kotun koli ana shirin yanke hukunci kan zaben Kano Hoto: Supreme Court Of Nigeria
Asali: Facebook

Majalisar dattawan ta amince da buƙatar Tinubu ta naɗa alkalan bayan nazari da karɓan rahoton kwamitin kula da harkokin shari'a da kare haƙkin dan adam a zaman ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun farko shugaba Tinubu ya buƙaci amincewar majalisar domin cike gurbin alkalan da suka rasu da kuma waɗanda suka yi murabus daga aiki.

Ma'aikatar shari'a ta ƙasa (NJC) ce ta shawarci Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa waɗanda zasu cike guraben.

Jerin alkalai 11 da majalisar ta amince da su

Legit Hausa ta tattaro muku sunayen sabbin alkalan da majalisar dattawa ta amince da su;

1. Mai shari'a Haruna Tsammani (arewa maso gabas), wanda ya jagoranci kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa.

2. Mai shari'a Moore Adumein (Kudu maso Kudu)

3. Mai shari'a Jummai Sankey (Arewa ta Tsakiya)

4. Mai shari'a hidiebere Uwa (Kudu maso Gabas)

Kara karanta wannan

Majalisar dokokin jihar Sokoto ta kamo hanyar magance matsalar tsaro a jihar bayan ta yi wani abu 1

5. Mai shari'a Chioma Nwosu-Iheme (Kudu maso Gabas)

6. Mai shari'a Obande Ogbuinya (Kudu maso Gabas)

7. Mai shari'a Stephen Adah (Arewa ta Tsakiya),

8. Mai shari'a Habeeb Abiru (Kudu maso Yamma)

9. Jamilu Tukur (Arewa maso Yamma)

10. Mai shari'a Abubakar Umar (Arewa maso Yamma)

11. Mai shari'a Mohammed Idris (Arewa ta Tsakiya).

Shugaban kwamitin, Sanata Tahir Monguno (APC, Borno), shi ne ya gabatar da rahoton a zaman majalisar na yau Alhamis, 21 ga watan Disamba, 2023, cewar Channels tv.

Ya ce wadanda aka nada suna da abubuwan da ake bukata da kuma gogewar da ake bukata domin cike guraben, kuma babu wani ƙorafi da aka shigar a kansu.

An yi yunkurin ƙona gidan gwamnatin Kano

A wani rahoton na daban Rundunar yan sandan Najeriya ta tabbatar da cewa wasu mutane sun yi ƙoƙarin babbake gidan gwamnatin jihar Kano.

Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Gumel ne ya bayyana haka yayin da ake dakon hukuncin kotun ƙoli kan zaben Gwamna Abba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel