Jerin Garuruwan da Matafiya Za Su Samu Ragin 50% da Zababbun Kamfanonin Sufuri da ke Cikin Tsarin
- Gwamnatin tarayya ta fitar da jerin garuruwan da matafiya za su ci moriyar rangwamen 50% na kudin mota kamar yadda Shugaban kasa Tinubu ya yi alkawari
- A cewar fadar shugaban kasa, matafiyan da ke amfani da hanyar jirgin kasa na gwamnatin tarayya za su yi amfani da jirgin a kyauta
- Fadar shugaban kasar ta kuma jaddada cewar wannan tagomashi zai ci gaba tsakanin Alhamis, 21 ga watan Disamba zuwa 4 ga watan Janairu
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
FCT, Abuja – Gwamnatin tarayya ta saki jerin garuruwan da matafiya za su iya samun ragin kaso 50 cikin dari na kudin mota.
Wannan ya yi daidai da alkawarin da Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi na rage kudaden motar zuwa garuruwa da kaso 50 yayin da matafiyan da ke amfani da jirgin kasa za su shiga a kyauta.
Tsawon wani lokaci za a dauka ana rangwamen 50% na kudin mota?
A cewar gwamnatin, ragin na Kirsimeti da sabuwar shekara zai ci gaba tsakanin 21 ga watan Disamba 2023 da 4 ga watan Janairun 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A safiyar ranar Alhamis, 21 ga watan Disamba, Bayo Onanuga, mai ba shugaban kasa Tinubu shawara na musamman kan labarai da dabaru, ya saki jerin garuruwa 28 da wannan tagomashin zai shafe.
Fadar shugaban kasar ta kuma saki jerin kamfanonin sufurin da suka yi hadaka da sabuwar gwamnatin.
Jerin kamfanonin sufurin da za a samu rangawamen kaso 50 na gwamnatin tarayya
- God is Good (GIG)
- Chisco Transport
- Young Shall Grow
- God Bless Ezenwata
- Area Motor
Jerin garuruwan da za a samu ragin 50% yayin bikin Kirsimeti
- Lagos zuwa Kano
- Lagos zuwa Abuja
- Lagos zuwa Kaduna-Zaria
- Lagos zuwa Jos
- Lagos zuwa Enugu
- Lagos zuwa Onitsha
- Lagos zuwa Owerri
- Lagos zuwa Aba
- Lagos zuwa Abakaliki
- Lagos zuwa Nsukka
- Lagos zuwa Uyo
- Lagos zuwa Port Harcourt
- Onitsha zuwa Kano
- Onitsha zuwa Lagos
- Onitsha zuwa Jos
- Onitsha zuwa Abuja
- Onitsha zuwa Sokoto
- Onitsha zuwa Gombe
- Onitsha zuwa Zakibiam
- Port Harcourt zuwa Owerri-Abba-Kano
- Abba zuwa Owerri-Abuja
- Abba zuwa Lagos
- Abuja zuwa Sokoto
- Abuja zuwa Lagos
- Abuja zuwa Onitsha-Owerri-Port Harcourt
- Abuja zuwa Enugu/Abakaliki
- Abuja zuwa Gombe
- Abuja zuwa Kano
Kalli jerin a kasa:
NRC ta sanar da jigilar mutane kyauta
A wani labarin, mun ji cewa hukumar kula da harkokin sufurin jiragen kasa ta Najeriya (NRC) ta ayyana fara jigilar fasinjoji kyauta daga ranar Alhamis, 21 ga watan Disamba.
Wannan ya biyo bayan umurnin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, wanda ya kuma amince da ragewa matafiya kudin mota da kaso 50 cikin dari domin mutane su samu damar zuwa hutun Kirsimeti da sabuwar shekara.
Asali: Legit.ng