Hukumar EFCC Ta Dauki Mataki Na Gaba Bayan Ta Cafke Tsohon Minista

Hukumar EFCC Ta Dauki Mataki Na Gaba Bayan Ta Cafke Tsohon Minista

  • Hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta’annati (EFCC) ta bayar da belin tsohon ministan wutar lantarki, Olu Agunloye, mako guda bayan tsare shi
  • Makonnin da suka gabata, EFCC ta bayyana tana neman Agunloye bisa zargin almundahanar dala biliyan 6 da ke da alaƙa da aikin samar da wutar lantarki na Mambilla da ake cece-kuce a kai
  • Agunloye ya kasance minista a gwamnatin shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo (1999-2003), kuma ya kasance a tsakiyar cece-kuce game da aikin Mambilla

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta EFCC ta bayar da belin tsohon ministan wutar lantarki, Olu Agunloye.

Kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito, an saki Agunloye bayan shafe mako guda yana tsare.

Kara karanta wannan

Shugaban EFCC ya bayyana kabilar da ta yi fice wajen cin hanci a Najeriya

EFCC ta saki Olu Agunloye
Hukumar EFCC ta bayar da belin Olu Agunloye Hoto: @bisifolutile
Asali: Twitter

An saki Agunloye na wani ɗan lokaci

Kakakin hukumar EFCC, Dele Oyewale, ya tabbatar da sakin Agunloye a ranar Laraba, 20 ga watan Disamba, rahoton The Punch ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ku tuna cewa hukumar EFCC na neman Agunloye ne makonnin da suka gabata bisa zarginsa da hannu a baɗakalar dala biliyan 6 da ake alaƙantawa da aikin samar da wutar lantarki na Mambilla.

Tsohon ministan bisa radin kansa ya miƙa kansa ga hukumar domin amsa tambayoyi a ranar 13 ga watan Disamba, kwana guda bayan sanarwar.

Agunloye ya riƙe muƙamin minista a lokacin shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo (1999-2003) kuma yana da alaƙa da aikin Mambilla mai cike da cece-kuce.

Obasanjo ya zarge shi da laifin bayar da kwangilar aikin ba tare da amincewar majalisar zartaswa ta tarayya (FEC) ba.

Agunloye dai ya musanta zargin, yana mai cewa Obasanjo baya faɗin gaskiya.

Kara karanta wannan

EFCC ta tabbatar da cewa tsohon Minista da ta ke nema ruwa a jallo ya shiga komarta, ta yi bayani

EFCC na neman Agunloye ruwa a jallo

Hukumar EFCC ta ayyana Olu Agunloye, tsohon ministan lantarki a matsayin wanda take nema ruwa a jallo kan zargin rashawa.

A cikin wata sanarwa da hukumar EFCC ta fitar, ta buƙaci ƴan Najeriya su sanar da hukuma mafi kusa idan sun ci karo da shi.

Obasanja Zai Bayar da Shaida Kan Agunloye

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya sanar da cewa a shirye yake ya bayar da shaida kan tsohon ministan lantarki, Olu Agunloye wanda ake nema ruwa a jallo kan zargin rashawa.

Agunloye wanda ya yi aiki a gwamnatin Obasanjo daga 1999 zuwa 2003, ana nemansa ne kan badaƙalar kwangilar Mambilla ta dala biliyan 6.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng