Kotun Koli Na Shirin Yanke Hukunci, Wasu Tsageru Sun Yi Yunƙurin Kona Gidan Gwamnatin Kano
- Rundunar yan sandan Najeriya ta tabbatar da cewa wasu mutane sun yi ƙoƙarin babbake gidan gwamnatin jihar Kano
- Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Gumel ne ya bayyana haka yayin da ake dakon hukuncin kotun ƙoli kan zaben Gwamna Abba
- Ya ce tuni suka kama wasu da ake zargi kuma sun maka su a kotun Abuja, kuma ya aike da saƙo ga ƴan siyasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Rundunar ƴan sandan Najeriya ta bankaɗo wani yunƙuri na ƙona gidan gwamnatin jihar Kano da wasu tsagerun mutane suka ƙulla, jaridar Leadership ta ruwaito.
Ƴan sanda sun gano wannan mummunan nufi ne yayin da kotun koli ta fara sauraron shari'a kan zaben gwamnan jihar Kani tsakanin APC da NNPP.
Kwamishinan ƴan sanda na jihar Kano, Muhammad Usaini Gumel, shi ne ya bayyana haka yayin ganawa da shugabannin midiya ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
CP Gumel ya bukaci kafafen yaɗa labarai su sanar da al'umma halin da ake ciki, yana mai cewa tuni suka shigar da ƙara a babban birnin tarayya Abuja kan lamarin.
A kalamansa, kwamishinan 'yan sandan ya ce:
"A zahirin gaskiya zaman lafiyan da muke jin daɗin mun samu a jihar nan, wasu ɓata gari sun yi yunkurin kawo masa cikas a lokuta daban-daban."
"Amma kuma bisa nasara a duk lokacin da irin haka ta faru, muna samun nasarar daƙile kowane yunƙuri mu shawo kan lamarin."
Wane mataki yan sanda suka ɗauka?
Da yake bayanin halin da ake ciki da matakan da jami'an tsaro suka ɗauka, CP Gumel ya ce sun kama waɗanda ake zargi, da masu fake wa da zanga-zanga suna sace-sace.
CP Gumel ya ci gaba da cewa:
“Ina amfani da wannan dama wajen kira ga ‘yan siyasa da su bi yarjejeniyar zaman lafiyar da suka sa ma hannu domin amfanin jama’a, kada su haifar da hargitsi a Kano."
An kai hari kan masu shirin bukukuwan kirsimeti
A wani rahoton na daban kuma Yan bindiga sun kai sabon hari mai muni kan mutane yayin da suke shirin zuwa kirsimeti a jihar Filato.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun halaka wani matashi ɗan shekara 19, sannan sun jikkata wasu mutum biyu.
Asali: Legit.ng