Hukumar NRC Ta Sanar da Fara Jigilar Yan Najeriya Kyauta Saboda Bikin Kirsimeti da Sabuwar Shekara
- Yan Najeriya za su amfana sosai daga gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Bola Tinubu gabannin hutun Kirsimeti da sabuwar shekara
- Hakan na zuwa ne yayin da hukumar sufurin jirgin kasa ta sanar da fara jigilar mutane kyauta daga ranar Alhamis, 21 ga watan Disamba, zuwa 4 ga watan Janairun 2023
- Hukumar NRC ta sanar da hakan ne don aiwatar da umurnin Tinubu na ragewa matafiya kaso 50 cikin dari na kudaden mota
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Hukumar kula da harkokin sufurin jiragen kasa ta Najeriya (NRC) ta ayyana fara jigilar fasinjoji kyauta daga ranar Alhamis, 21 ga watan Disamba.
Wannan ya biyo bayan umurnin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, wanda ya kuma amince da ragewa matafiya kudin mota da kaso 50 cikin dari domin mutane su samu damar zuwa hutun Kirsimeti da sabuwar shekara.
Hukumar NRC a cikin sanarwar ta ce biyo bayan umurnin Tinubu, za ta fara jigilar fasinjoji kyauta daga ranar Alhamis, 21 ga watan Disamba, 2023 zuwa Alhamis, 4 ga watan Janairun 2024, rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta kara da cewa:
“An shawarci fasinjoji da su karbi tikitinsu na kyauta ta dandalin siyan tikiti na yanar gizo. Ba za a raba tikiti a tashoshin jiragen kasa ba. Don Allah a lura cewa babu matafiyin da za a bari ya shiga jirgin kasan ba tare da tikiti ba.
“Muna umurtan matafiyan da su shirya kansu, su yi biyayya ga jami’an tsaro da ka’idojin hukumar NRC da na jami’anta yayin da suke tashar jirgin kasan da kuma cikin jirgin kasan. Muna yi wa dukkan kwastamominmu barka da bikin Kirsimeti da sabuwar shekara mai zuwa.
Cross River ta ba da hutun kwana 14
A wani labarin, mun ji cewa gwamnan jihar Cross River, Bassey Otu, ya amince da tsawaita hutun ma'aikatan gwamnati a jihar.
Gwamnan a cikin wata sanarwa da babban sakataren labaransa, Emmanuel Ogbeche ya saki ya amince da Laraba, 20 ga watan Disamba zuwa Talata, 2 ga watan Janairun 2024, a matsayin hutu, illa ga wadanda ke ayyuka na musamman, AIT ta rahoto.
Asali: Legit.ng