Shugaban EFCC Ya Bayyana Kabilar da Ta Yi Fice Wajen Cin Hanci a Najeriya

Shugaban EFCC Ya Bayyana Kabilar da Ta Yi Fice Wajen Cin Hanci a Najeriya

  • Matsalar cin hanci da rashawa ta daɗe ana fama da ita a ƙasar nan inda ta riga ta zama ruwan dare
  • Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ya yi tsokaci kan matsalar inda ya bayyana cewa matsalar ba ta nuna bambancin addini ko ƙabila
  • A cewar shugaban masu satar dukiyar ƙasar nan sun fito daga dukkanin addinai da ƙabilun ƙasar nan inda ya yi kira da a daina sanya ƙabilanci a yaƙi da cin hanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Shugaban hukumar yaƙi da yi wa tattalin arzikin ƙasa ta’annati (EFCC), Ola Olukoyede, ya ce cin hanci da rashawa ba shi da ƙabila ko addini, saboda Musulmai da Kirista suna satar dukiyar al’umma.

Kara karanta wannan

Atiku ya taso Tinubu a gaba, ya yi masa wankin babban bargo kan abu 1

Olukoyede ya bayyana haka ne a wani taron bita na kwanaki biyu da hukumar ta shirya tare da ma’aikatar ƙananan hukumomin jihar Kaduna a ranar Talata a Kaduna, cewar rahoton Daily Trust.

Shugaban EFCC ya yi magana kan cin hanci
Olukoyede ya yi tsokaci kan matsalar cin hanci a Najeriya Hoto: EFCC Nigeria
Asali: Twitter

Jaridar The Punch ta ce Olukoyede wanda ya samu wakilcin A’isha Abubakar, kwamandan hukumar EFCC ta shiyyar Kaduna, ya bayyana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mutanen da ke satar dukiyar Najeriya Kiristoci ne da Musulmai. Ba yaƙi ne tsakanin addinai ba, kuma yaƙi da cin hanci da rashawa ba ya tsakanin ƙabilu”.
"Abin da muke faɗa a ƙasar nan yaƙi ne tsakanin nagarta da mugunta, yaƙin gama-gari ne ga domin ceto Najeriya, yaƙi ne domin masu tasowa da waɗanda ba a haifa ba, tabbas yaƙi ne domin kyawun goben nahiyar Afirika."

Wacce buƙata ya nema a wajen ƴan Najeriya?

Olukoyede ya cigaba da cewa:

Kara karanta wannan

"Dalilin da ya sa na kulla yarjejeniya 8 da Wike", Gwamna Fubara Ya Magantu

"Kada mu samar da yanayin da idan muka hukunta mutane saboda sun aikata cin hanci da rashawa, za mu ba su kariya saboda sun fito daga ƙabilunmu."
"Yunƙurin tabbatar da cewa ba mu samar da wani yanayi da cin hanci zai mamaye al’ummarmu ba, abu ne na kowa da kowa."
"Bai kamata a bar wa EFCC da sauran hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa kaɗai ba. A kan hakan ne na sake jaddada buƙatar farawa daga tushe, wato kananan hukumomi, wajen yaƙi da cin hanci da rashawa."

EFCC Ta Cafke Tsohon Minista

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'annati (EFCC) tabbatar da cewa tsohon ministan wutar lantarki ya shiga hannunta.

Wanda ake zargin, Olu Ogunloye ya shiga hannun hukumar ne kwanaki kaɗan bayan an ayyana shi a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng