“N70,000 Ne Kudin Biza”, Budurwa Ta Nuna Wa ’Yan Najeriya Yadda Za Su Je Kasar Norway da Kudi Kadan
- Wata ‘yar Najeriya ta ce naira 170,000 ne za ka biya kudin bizar zuwa Norway, kuma ta fada wa mutane yadda ake samun takardar
- Grandma Shasha ta ce kudin neman bizar kasar Norway bai da tsada, Euro 80 ko naira 72,000 ne kawai
- Ta ce akwai bukatar mutum ya nuna shaidar yana da kudi, kasuwanci mai rijista ko kuma shaidar takardar aiki domin samun bizar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Wata matashiya ta shawarci mutane kan yadda ake samun biza zuwa kasar Norway da kuma yadda mutum zai yi kaura zuwa kasar ta Schengen.
Mai ba da shawara kan tafiye-tafiyen, Grandma Shasha, ta lura cewa biza zuwa Norway yana kai kusan naira 72,000 ne kawai a kudin Najeriya
Ta ce sauran cajin kudade na takardu da wasu ayyukan na iya kai kudin zuwa naira 170,000 ga masu neman bizar ziyara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abin da ofishin jakadancin Norway a Najeriya ya ce kan kudin biza
Baya ga bizar, ta ce matafiya za su gabatar da shaidar wadatattun kudi a cikin asusun bankinsu, da kuma tsarin tafiyarsu.
A cewar ofishin jakadancin Norway a Najeriya, takardar bizar baki da ta kai Yuro dubu 72, tana ba mai ita damar zama a Norway ko wasu kasashe na yankin Schengen na tsawon kwanaki 90 a cikin kwanaki 180.
Sabanin bizar baki wacce ke da arha, shafin neman takardar bizar kasar ya nuna cewa takardar izinin zama ko bizar aiki na kai kusan naira dubu 506.
Kalli bidiyonta a kasa:
Gwamnatin Birtaniya ta ba 'yan Najeriya damar neman tallafin karatu
A wani labarin, dalibai daga kasashe akalla goma sha hudu da suka had da Najeriya sun samu damar neman kudin tallafin karatu daga babbar gidauniyar GREAT a zangon karatu na 2024-25.
Tallafin zai ba daliban Najeriya da sauran kasashen damar samun Euro 10,000 don biyan kudin makaranta a shirye-shiryen karatu na matakin PGD a wasu jami'o'i goma sha bakwai na Birtaniya.
Akwai guraben karatu 210 da jami'o'i 71 ke bayarwa a duk faɗin Ingila, Wales, Scotland da Ireland ta Arewa.
Asali: Legit.ng