Kungiyar Kwadago Ta Kasa Ta Yi Wa Shugaba Tinubu da CBN Babbar Barazana Kan Abu 1 Tak

Kungiyar Kwadago Ta Kasa Ta Yi Wa Shugaba Tinubu da CBN Babbar Barazana Kan Abu 1 Tak

  • Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Bola Tinubu da kuma CBN sun samu barazanar wata gagarumar zanga-zanga daga shugaban NLC na ƙasa, Joe Ajaero
  • Ajaero, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce babbar zanga-zangar da za ayi na nan tafe idan Tinubu da CBN suka gaza magance matsalar ƙarancin kuɗi da ke addabar ƙasar nan a halin yanzu
  • Shugaban NLC ya ce bai kamata ƴan Najeriya su sake fuskantar matsalar ƙarancin kuɗi ba kamar yadda suka yi a farkon wannan shekarar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta yi wa shugaban ƙasa Bola Tinubu da babban bankin Najeriya (CBN) barazana kan ƙarancin kuɗaɗe a bankunan Najeriya.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta bayyana matsayarta kan yarjejeniya 8 da Tinubu ya cimmawa tsakanin Wike da Fubara

A yayin cigaba da fuskantar zuwan bukukuwan Kirsimeti, shugaban ƙungiyar NLC na ƙasa, Joe Ajaero, a wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana irin illar da lamarin ke da shi ga ƴan Najeriya, cewar rahoton Daily Trust.

Kungiyar NLC ta gargadi Tinubu da CBN
Joe Ajaero ya bukaci Tinubu ya kawo karshen matsalar karancin kudi Hoto: NLC, Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Ajaero ya yi kira ga gwamnati da ta ɗauki matakin gaggawa domin shawo kan lamarin, inji rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NLC ta gargadi Tinubu, CBN

A baya-bayan nan dai ƴan Najeriya sun koka kan rashin samun kuɗaɗe a bankuna domin biyan bukatunsu na yau da kullum duk kuwa da tabbacin da CBN ta yi na shawo kan lamarin.

Bankunan sun kasance suna ba da kuɗi a kan kanta, kuma yawancin injinan biyan kuɗi na ATM ba sa bayar da kuɗi.

Sai dai ƙungiyar ta NLC a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce ya kamata gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Tinubu da CBN su yi tsammanin samun zanga-zanga idan har ba ayi abin da ya dace ba domin magance matsalar ƙarancin kuɗin ba.

Kara karanta wannan

Wike vs Fubara: Jerin yan siyasan da suka sanya hannu a yarjejeniya kawo karshen rikicin Rivers

'Ƴan Najeriya ba za su sake amincewa da ƙarancin kuɗi ba', NLC

Ajaero ya cigaba da cewa, "manufar sake fasalin kudin da ba ta dace ba kwata-kwata" da ƴan Najeriya suka ɗanɗana a farkon wannan shekarar har yanzu tana cikin zukatansu, kuma ba za su amince da sake fuskantar ƙarancin kuɗi ba.

Shugaban NLC ya ce babu dalilin da zai sa ƴan Najeriya su shiga cikin mawuyacin hali irin na ƙarancin kuɗi a shekarar 2023, inda ya ce gwamnati da CBN ba su da wani uzuri da za su ba jama'a.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Mun ji dalilai irin su akwai ƙaruwar takardun kuɗi na bogi da kuma ɓoye kuɗin. Waɗannan dalilan ba abin yarda ba ne domin ba mu ga wani dalili da zai sanya wani ɗan Najeriya ya ɓoye kuɗi ba. Koma dai menene ba talakan Najeriya ne ke ɓoye kuɗi a gidajensu ba."

Kara karanta wannan

Tinubu ya dauki mataki bayan babban minista ya yi murabus

NLC Ta Musanta Shiga Yajin Aiki

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) da ƙungiyar ƴan kasuwa ta musanta batun shiga yajin aiki.

Shugabannin NLC da TUC sun shaida cewa takardar da ake yadawa a kan maganar shiga yajin-aiki sam ba daga hannunsa ta fito ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng