Babban Hafsan Tsaro CDS Ya Faɗi Halin da Ake Ciki a Bincike Kan Jefa Bam a Taron Musulmai a Kaduna

Babban Hafsan Tsaro CDS Ya Faɗi Halin da Ake Ciki a Bincike Kan Jefa Bam a Taron Musulmai a Kaduna

  • CDS Christopher Musa ya bayyana inda aka kwana a bincike kan harin bama-baman da sojoji suka kai a taron Musulmi a Kaduna
  • Babban hafsan tsaron ya ce nan ba da jimawa ba za a sanar da sakamkon binciken domin kowa ya san abin da ya faru
  • Akalla mutane 100 suka kwanta dama yayin da jirgin soji ya jefa bam sau biyu a taron bikin Maulidi a Tudun Biri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Babban Hafsan Tsaro na ƙasa, Janar Christopher Musa, ya tabbatar da cewa rahoton binciken da aka yi kan harin bama-baman Kaduna zai fito nan ba da daɗewa ba.

CDS ya kuma ƙara tabbatarwa yan Najeriya cewa da zaran rahoton binciken ya kammalu, za a bayyana shi kowa ya san gaskiyar abin da ya faru a kauyen Tudun Biri.

Kara karanta wannan

"Larabci harshe ne da ba na biyunsa", Zulum zai gina makarantun Islama guda 27 a Borno

Babban hafsan tsaro na ƙasa, CDS Musa.
Nan bada dadewa ba rahoton harin bama-baman Kaduda zai bayyana, CDS Musa Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Babban hafsan tsaron ya bayyana haka ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels ranar Talata, 19 ga watan Disamba, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

CDS ya kuma fahimci damuwar jama'a tare da jaddada kudirin gwamnati na bankado gaskiyar lamarin da ya faru.

Za a bayyana abinda aka gano kowa ya sani - CDS

A kalamansa ya ce:

"Gwamnatin Tarayya ta kafa kwamiti da zai gudanar da bincike kan lamarin. Mun san cewa a karshe, gaskiya za ta yi halinta kuma kowa zai fahimci cewa tabbas kuskure ne."

Daily Trust ya tattaro cewa kusan Musulami 100 ne suka rasa rayukansu yayin da jirgin sojoji ya saki ruwan bama-bamai a kauyen Tudun Biri da ke jihar Kaduna.

Harin wanda rundunar soji ta ce ba da gangan ta yi ba, ya kuma jikkata wasu da dama yayin da suke tsaka da bikin Maulidi ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Matashi ya yi cuku-cukun fita daga talauci, ya kera katafaren gida na alfarma da siyan mota

Rundunar sojin kasa ta Najeriya dai ta nemi afuwar al'umma tana mai cewa bisa kusƙure sojoji suka jefa bam din kuma ƴan ta'adda ne asalik abin harinsu.

Amma masu ruwa da tsaki da dama sun yi kira da a gudanar da cikakken bincike tare da hukunta wadanda aka samu da laifi.

Shin da yiwuwar a yi rufa-rufa a binciken?

Da yake jawabi game da damuwa kan yuwuwar yin rufa-rufa, CDS ya sake nanata kudirin gwamnati na yin komai a buɗe, yana mai cewa "za a bayyana binciken ga yan Najeriya."

"Gwamnatin tarayya ce ke jan ragamar binciken kuma tana kan aiki, ina da tabbacin nan bada jimawa ba za a sanar da abinda aka gano."

Ƙotun ɗaukaka kara ta yanke hukunci kan nasarar Sanatoci 2

A wani rahoton kuma Sanata Aliyu Wamakko da Aminu Tambuwal sun san makomarsu a kotun ɗaukaka kara ranar Talata.

Kotun ta tabbatar da nasarar tsoffin gwamnonin jihar Sakkwato guda biyu a matsayin sanatan Sokoto ta kudu da arewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262