Dakarun Sojoji Sun Samu Manyan Nasarori 2 Kan Yan Bindiga a Jihar Zamfara
- Sojoji sun samu nasara babba a yakin da suke da yan bindiga a jihar Zamfara da ke shiyyar Arewa maso Yammacin Najeriya
- Kakakin rundunar Operation Hadarin Daji ya ce sojojin sun ceto mutum 13 da aka sace, sun tarwatsa sansanonin yan ta'adda
- Dakarun sun kuma kama wasu yan ta'adda 11 da ake zargin su da siyarwa ƙasurgumin ɗan bindiga kayan aiki
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Zamfara - Dakarun rundunar hadin gwiwa dake shiyyar Arewa maso Yamma, Operation Hadarin Daji (OPHD), sun yi nasarar ceto mutane 13 da aka yi garkuwa da su.
Haka nan kuma dakarun sojojin sun samu nasarar damƙe mutane 11 da ake zargin suna kaiwa kasurgumin ɗan bindiga kayan aiki da makamai duk a jihar Zamfara.
Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin OPHD, Kaftin Ibrahim Yahaya, ya fitar ranar Litinin kuma hukumar soji ta wallafa a shafinta na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce rundunar sojin hadin gwiwa, ranar 17 ga watan Disamba, 2023, sun fita sintirin bincike da ceto a yankin Gobirawan Chali da Dangulbi da ke kan titin Dansadau a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.
A cewarsa, yayin wannan samame ne sojojin suka ceto mutane 13 da aka sace, waɗanda ƴan ta'adda suka barsu, suka ranta a na kare da daren ranar Lahadi.
Kakakin rundunar ya kuma bayyana cewa dukkan waɗanda sojojin suka ceto sun fito ne daga ƙauyen Mutunji, yankin Masarautar Ɗansadau a ƙaramar hukumar Maru.
Wane hali waɗanda aka ceto suke ciki?
A halin yanzu sojojin sun kai su asibiti domin gwada lafiyarsu gabanin a miƙa su ga danginsu.
A sanarwan wadda rundunar sojin kasa ta wallafa a shafinta, Kaftin Yahaya ya ce:
"Dukkan wadanda aka ceto an mika su ga wakilin gwamnatin jihar Zamfara domin hada su da iyalansu."
“Rundunar sojojin sun kuma tarwatsa mafakar manyan hatsabiban ‘yan ta’adda a kauyen Gidan Jaja a karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.”
Rundunar ta OPHD ta kama wasu mutane 11 da ake zargin suna sayar da kayan aiki ga wani fitaccen dan ta’adda, Halilu Sububu, a Kwanar Boko, karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.
Wani mazaunin yankin ƙaramar hukumar Zurmi a Zamfara ya ce a gaskiya koda sojoji na samun wannan nasara babu abinda ke sauya wa kan hare-haren da ake kai masu.
Mutumin wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda halin tsaro ya shaida wa Legit Hausa cewa:
"Ku san kowace zaka ga sojoji na cewa sun samu nasara, amma sai kaje Zamfara zaka gane abun ba ya sauya zani, musamman yankin Zurmi, mu kan kewaye muke da su."
"Ni a ganina ya kamata jami'an tsaro su kara dagewa, suna kokari domin wani lokacin fin ƙarfinsu ake, ko a kwanan baya sojoji sun kawo ɗauki amma yan ta'addan sun nunka su."
Ya ƙara da cewa sun barwa Allah komai domin babu zaluncin da yake ɗorewa a duniya.
Dakarun sojoji sun tarwatsa mafakar hatsabiban yan bindiga
A wani rahoton kuma Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar tarwatsa mafakar ƙasurguman 'yan bindiga a jihohin Zamfara da Sokoto.
Kakakin rundunar Operation Hadarin Daji, Kaftin Yahaya Ibrahim, ya ce sojojin sun halaka yan bindiga biyar, sun kwato makami.
Asali: Legit.ng