Babban Hafsan Tsaron Ƙasa CDS Zai Tona Asirin Wasu Jiga-Jigan Masu Laifi a Najeriya

Babban Hafsan Tsaron Ƙasa CDS Zai Tona Asirin Wasu Jiga-Jigan Masu Laifi a Najeriya

  • CDS Christopher Musa ya sha alwashin tona asirin duk wanda ya gano da hannu a harƙallar miyagun kwayoyi a Najeriya
  • Babban hafsan tsaron ya ɗauki wannan alƙawarin ne yayin ganawa da shugaban NDLEA na ƙasa, Buba Marwa a Abuja ranar Litinin
  • Ya kuma ƙara bai wa hukumar NDLEA tabbacin cewa rundunar soji za ta ci gaba da taimakawa wajen kawo karshen ta'amali da kwayoyi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Babban hafsan hafsoshin tsaron ƙasa (CDS), Janar Christopher Musa, na ganawa yanzu haka da shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA), Buba Marwa.

Babban hafsan tsaro, Manji Janar Christopher Musa.
CDS ya lashi takobin tona asirin masu harkallan miyagun kwayoyi a Najeriya Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta tattaro cewa taron na gudana a hedkwatar hukumar NDLEA ta ƙasa da ke Area 11, Garki a babban birnin tarayya Abuja ranar Litinin, 18 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da wasu tsageru suka farmaki hukumar gwamnati a Abuja, sahihan bayanai sun fito

Babban hafsan tsaron, CDS Musa ya kuma baiwa hukumar NDLEA tabbacin cewa zai taimaka wajen bankado masu safarar muggan kwayoyi da masu cin zarafi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan shi ne karo na farko da babban hafsan tsaro da shugaban NDLEA, Manjo Janar Buba Marwa mai ritaya, suka haɗu suka tattauna a hukumance.

CDS ya ɗauki alƙawarin taimakawa NDLEA

Yayin wannan ganawa, CDS ya yi tir da yadda safarar miyagun kwayoyi da cin zarafi ƙe karuwa a faɗin sassan Najeriya.

Haka nan kuma ya yaba tare jinjinawa Marwa bisa yadda yake kokarin tsamo Najeriya da tsaftace ƙasar daga duk abinda ya shafi harƙalla da miyagun kwayoyi.

Ya kuma yi alkawarin cewa rundunar sojojin Najeriya za su ci gaba da bayar da goyon baya ga hukumar ta NDLEA mai fafutukar kawo ƙarshen ta'amali da haramtattun kwayoyi.

Kara karanta wannan

An bankado wata kullalliya da gwamnatin Tinubu take yi wa Peter Obi

CDS ya jaddada cewa rundunar soji ba zata kare ko ɗaga wa duk wanda ta kama da miyagun kwayoyi ƙafa ba.

Tsohon shugaban NSIB ya yi magana mai jan hankali

Kuna da labarin Tsohon shugaban hukumar NSIB da aka tsige ya bayyana yadda aurensa ya rushe da wahalar da ya sha saboda kokarin yin gaskiya a bakin aiki.

Injiniya Akin Olateru, wanda tun 2017 yake kan kujerar, ya ce ba ya kishi da sabon wanda zai gaje shi saboda aikin ba ƙarami bane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262