"Sakin Bam Bisa Kuskure": Lauya Ya Magantu Kan Abin Da Tinubu Ya Dace Ya Yi Wa Mazauna Kauyen Kaduna
- An bukaci Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar cewa an cika dukkan alkawuran da aka yi wa wadanda bama-baman sojoji da aka saki a kauyen Kaduna bisa kuskure ya shafa
- Ismail Balogun, wani fitaccen lauya, yayin wannan kirar ya fada wa Legit.ng cewa afkuwar lamarin ya nuna yadda abubuwa suka tabarbare a Najeriya
- Kwararen lauyan ya koka kan gazawar gwamnati wurin kare rayyuka da dukiyoyin talakawan Najeriya
Tudun Biri, Jihar Kaduna - An bukaci gwamnatin tarayya - karkashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta cika dukkan alkawurran da ta yi wa wadanda bama-baman da aka saki bisa kuskure ya shafa a Kaduna.
Ismail Balogun, wani lauya, wanda ya yi magana da Legit.ng ya yi tir da harin jirgin saman da sojojin Najeriya suka kai, ya kara da cewa babu wani diyya da zai iya maye gurbin rayyukan da aka rasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun saki bam kan mazauna kauyen Kaduna bisa kuskure
A kalla mutane 120 ne aka sakarwa bam bisa kuskure yayin wani samame da sojoji suka yi a Tudun Biri a karamar hukumar Igabi da ke Jihar Kaduna a ranar Talata, 5 ga watan Disamba.
Mutane yan Najeriya da dama sun yi tir da lamarin, ciki har da Shugaba Bola Tinubu da ministocinsa. Fadar shugaban kasa ta kuma yi alkawarin biyan diyya ga iyalan wadanda abin ya shafa.
Ba za a amince da kuskuren sakin bam ba - Balogun
Balogun ya kuma kara da cewa sakin bam bisa kuskure alama ne na kasa wacce ta gaza.
"Wannan wani alama ce na kasa da ta gaza, kuma abin takaici ne ganin irin wannan babban abin bakin cikin da ke faruwa a kasarmu. Ba za a amince da hakan ba, kuma ana tir da hakan," ya fadawa Legit.ng.
"Hakkin da ya rataya kan gwamnati na farko karkashin kundin tsarin mulki shine kiyayye rayuwa da dukiyoyin al'umma. Amma, akasin haka ke faruwa a kasarmu. Rayuwar talakawar Najeriya ba ta da ma'ana a wurin wadanda ke kula da kasar.
"Ina ganin babu wani adadin kudi da zai iya biyan iyalan wadanda suka rasu, duk da haka ana kira ga gwamnati ta yi gaggawar biyan diyya ga iyalan wadanda abin ya shafa."
Asali: Legit.ng