Kotu Ta Tisa Keyar Fitaccen Dillalin Miyagun Kwayoyi Zuwa Gidan Yari, Hotuna Sun Fito

Kotu Ta Tisa Keyar Fitaccen Dillalin Miyagun Kwayoyi Zuwa Gidan Yari, Hotuna Sun Fito

  • Babban Kotun Tarayya da ke Legas ta yanke wa dillalin miyagun kwayoyi Okenwa Chris Nzewi daurin shekara hudu a gidan yari da zabin biyan tarar naira miliyan 4
  • An kuma kwace katafaren gidan Nzewi na makuden miliyoyi an mika wa gwamnatin tarayyar Najeriya
  • An kuma yanke wa abokin harkalarsa Sunny Okeh Ukah daurin shekaru uku a gidan yari da zabin biyan tarar naira miliyan 3, an kuma umurci su da yin ayyukan yi wa al'umma hidima

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

Legas, Najeriya - Kotun Gwamnatin Tarayyar Najeriya da ke Legas ta yanke wa Okenwa Chris Nzewi, dilallin miyagun kwayoyi, daurin shekara hudu a gidan yari da zabin biyan tarar naira miliyan 4.

Wata sanarwa da Hukumar Yaki da Fatauci da Shan Miyagun Kwayoyi (NDLEA) ta fitar ya kuma nuna kotun ta bai wa gwamnatin tarayya ikon kwace katafaren gidan miliyoyin naira da ke Victoria Garden City (VGC) Estate, Lekki, Legas mallakinsa.

Kara karanta wannan

"Ɗana ke siyo min": An Kama Tsohuwa Mai Shekara 75 Kan Safarar Miyagun Kwayoyi a Legas

Kotu ta kwace katafaren gida mallakar fitaccen dilallin miyagun kwayoyi
NDLEA ta yi nasarar kwace katafaren gidan wani dilallin miyagun kwayoyi a Legas. Hoto: @ndlea_nigeria
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar ta NDLEA ta ce Nzewi ya yi amfani da katafaren gidansan a matsayin dakin gwaji don sarrafa miyagun kwaya na methamphetamine.

NDLEA ta samu abokin harkallar Nzewi da laifi

Hakazalika, Legit Hausa ta tattaro cewa an kama Nzewi tare da abokin harkallarsa, Sunny Okeh Ukah, a watan Yulin 2022.

Daga bisani an gurfanar da su a kotu a kara mai lamba FHC/L/527C/2022 a Babban Kotun Tarayya a Legas. Dukkansu biyu sun amsa laifinsu.

Kamar Nzewi, Ukah shima an same shi da laifi an kuma yanke masa daurin shekaru uku, dukkansu da zabin tarar naira miliyan 3.

An kuma bai wa Ukenwa da Ukah hukuncin aikin tallafawa al'umma na wata hudu da uku, kamar yadda aka jero.

An kuma bai wa gwamnatin tarayya motar Ukah mai lamba EKY 496 DJ.

Kara karanta wannan

Abba vs Gawuna: Jigon LP ta bayyana wanda ya kamata Kotun Koli ta ayyana a matsayin gwamnan Kano

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164