Gwamnan APC Zai Yi Wa Tsofaffi da Zawarawa Wani Muhimmin Abu 1
- Gwamnan jihar Ebonyi ya yi nuni da cewa gwamnatinsa za ta bayar da fifiko kan jindaɗin tsofaffi da zawarawa a jihar
- Gwamna Francis Nwifuru ya nanata cewa zai ba tsofaffin da zawarawan fifiko ne saboda yadda ya yaɓa da jajircewarsu wajen cigaban jihar
- Ya bayyana cewa halin matsin tattalin arziƙin da ake fama da shi a ƙasar nan ya tilasta cewa ya kamata a waiwayi jindaɗin tsofaffin da zawarawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Ebonyi - Gwamna Francis Nwifuru na Ebonyi ya nanata cewa gwamnatinsa za ta cigaba da ba da fifiko wajen kyautata rayuwar tsofaffi da zawarawa a jihar.
Nwifuru ya bada wannan tabbacin ne a cibiyar Christian Ecumenical da ke Abakaliki, a lokacin taron dattawa da zawarawa a Abakaliki, cewar rahoton PM News.
Gwamnan ya jaddada matsayinsa na kyautatawa jama’a musamman manya da zawarawa da sauran marasa galihu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya yabawa dattawan bisa jajircewarsu da gudunmawar da suke bayarwa wajen cigaban jihar.
Ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta cigaba da girmama tsofaffi da zawarawa.
"Idan muka girmama iyayenmu, Allah zai girmama mu." A cewarsa.
Gwamnan ya amince da halin da ake ciki na tattalin arziƙi a halin yanzu da kuma yadda hakan ya shafi matan da mazansu suka mutu da kuma tsofaffi, ya kuma yi alƙawarin duba jin daɗin su.
"Ina tabbatar muku cewa ina tare da ku, ina gare ku kuma zan yi muku aiki." A cewar gwamnan.
An buƙaci Nwifuru ya yi murabus
Ƴan asalin jihar a ƙarƙashin ƙungiyar Association of Ebonyi Indigenes Socio-Cultural in the Diaspora (AEISCID), sun nemi gwamnan jihar Francis Ogbonna Nwifuru, da ya yi murabus.
Ƙungiyar ta ƴan asalin jihar mazauna ƙasashen waje, ta zargi gwamnan da kasa taɓuka komai sai abinda magabacinsa, Dave Umahi, ya sanya shi.
Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Tabbatar da Nasarar Nwifuru
A wani labarin kuma, kun ji cewa kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da nasarar Gwamna Francis Nwifuru na jihar Ebonyi.
Kotun mai alƙalai uku sun kori ƙarar da Chukwuma Odii, da jam'iyyarsa ta PDP suka ɗaukaka kana suka tabbatar da nasarar Gwamna Nwifuru na jam'iyyar APC.
Asali: Legit.ng