Murna Yayin Da Gwamnati Ta Amince Da Karin Albashi Da Alawus Na Disamba Ga Ma'aikata

Murna Yayin Da Gwamnati Ta Amince Da Karin Albashi Da Alawus Na Disamba Ga Ma'aikata

  • Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya amince da biyan ƙarin N35,000 a albashin ma'aikatan jihar
  • Amincewar na ƙunshe ne a cikin wata takardar da shugaban ma’aikata na jihar Legas, Bode Agoro ya sanya wa hannu, mai lamba CIR/HOS/’23/Vol.1/109
  • Gwamnan ya kuma amince da biyan kashi 50% na albashin ma’aikata a matsayin alawus na ƙarshen shekara ga duk masu muƙamai na siyasa da ma’aikatan gwamnati

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Ikeja, jihar Legas - Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya amince da biyan ƙarin N35,000 a albashin ma’aikatan jihar.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito a ranar Asabar, 16 ga watan Disamba, hakan ya kasance a daidai lokacin da gwamnan Legas ya kuma amince da biyan kashi 50% na albashin ma’aikata a matsayin alawus na ƙarshen shekara ga duk masu muƙamai na siyasa da ma’aikatan gwamnati.

Kara karanta wannan

Gwamna Fubara ya so yin abu 1 kafin rikicinsa da Wike ya yi kamari

Sanwo-Olu ya yi karin albashi
Sanwo-Olu ya kara wa ma'aikata albashi a Legas Hoto: Babajide Sanwo-Olu
Asali: Facebook

Sauran sun haɗa da ma'aikatan ƙananan hukumomi, ma'aikatan hukumar ilmin bai ɗaya, da ma'aikatan hukumar Lagos Neighborhood Safety Corps (LNSC).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legas: Murna yayin da Sanwo-Olu ya amince da alawus

Amincewar na ƙunshe ne a wata takardar da ke ɗauke da sa hannun shugaban ma’aikatan jihar Legas, Bode Agoro.

Gwamnatin Legas ta amince da karin albashi ga ma'aikata
Takardar amincewar gwamnan kan karin albashin Hoto: @oyeniran_s
Asali: Twitter

Takardar ta bayyana cewa gwamnan ya amince da biyan kuɗaɗen ne a matsayin wani ɓangare na yabawa da gudummawar da ma’aikatan gwamnati ke bayarwa wajen cigaban jihar, da kuma jajircewarsa wajen kyautata rayuwarsu.

Bugu da ƙari, sanarwar ta lura cewa alawus ɗin na ƙarshen shekara da kuma ƙarin albashin wanda za a biya tare da albashin watan Disamba na 2023, ba zai zama mai haraji ba.

Obaseki Zai Biya Albashin Watan 13

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya sanar da ranar biyan albashin watan 13 ga ma'aikatan jihar.

Gwamnatin dai za ta biya albashin watan Disamba a ranar Litinin 11 ga watan Disamba, yayin da ma’aikata za su samu albashin watan 13 a ranar Laraba 27 ga watan Disamba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng