Hazikin Gwamna Ya Raba N450m Ga Makarantun Sakandare 100 a Jiharsa
- Gwamnan jihar Katsina ya yi wata muhimmiyar huɓɓada domin inganta harkokin ilmi a jihar
- Dikko Umaru Radda ya fitar da N450m domin ba makarantun sakandare 100 na jihar su bunƙasa harkokin koyarwa
- Gwamnan ya bayar da kuɗin yayin ƙaddamar da shirin AGILE kashi na biyu wanda aka yi a ƙaramar hukumar Bindawa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, a ranar Laraba ya raba Naira miliyan 450 ga makarantun sakandire 100 na jihar.
Gwamna Radda ya raba kuɗin ne a wani biki da aka gudanar a makarantar sakandaren gwamnati ta Doro a ƙaramar hukumar Bindawa inda ya ƙaddamar da kashi na biyu na shirin AGILE, cewar rahoton PM News.
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Radda ya jaddada ƙudirinsa na kawo cigaban ilimi a jihar ta hanyar gudanar da shirye-shirye da dama.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar da babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan jihar, Ibrahim Kaula Mohammed ya fitar ta bayyana cewa:
"Mallam Dikko Radda ya jaddada cewa shirin ba shi da wani mummunan tasiri a kan kyawawan dabi’un al’ummar jihar da kuma danginsu.”
Gwamna Radda ya yi muhimmin kira
Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su bijirewa duk wani tunani mara kyau da zai ƙara mayar da yankin Arewa koma baya.
Gwamna Radda ya ce tallafin da aka fitar a ƙarƙashin shirin AGILE rance ne da za a biya a cikin wani lokaci da aka ƙayyade.
Ya ce gwamnatin jihar ta fara shirye-shiryen zagaye na biyu na sake gina wasu makarantun sakandare 75 a jihar.
Da yake ƙarin haske kan shirin na AGILE, kodinetan, Dakta Mustapha Shehu, ya ce za a fara aikin kashi na biyu na sauran makarantun sakandare 75 a watan Janairun 2024 kuma za a kammala shi a kashi na uku na shekara.
Gwamna Radda Ya Biya Kudin NECO
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina ya amince da fitar da N977m domin biyan kuɗin jarabawar NECO.
Malam Dikko Umaru Radda ya amince da fitar da kuɗin ne domin biyan kuɗin jarabawar ga ɗalibai 48,385 da suka zana jarabawar a faɗin jihar.
Asali: Legit.ng