“Alamomin Zuwan Karshen Duniya”: Malamin Addini Ya Yi Hasashen Abun da Zai Faru a 2024

“Alamomin Zuwan Karshen Duniya”: Malamin Addini Ya Yi Hasashen Abun da Zai Faru a 2024

  • Fasto Joshua Iginla, wanda ya kafa majami'ar Joshua Iginla Ministries, ya yi hasashen abun da ya ce zai faru a tsakanin 2024 da 2026
  • Limamin ya koka kan sauyin yanayi, inda ya ce 'masana kimiyya za su ba mu fassarar abin da suke tunanin shine'
  • Fasto Joshua Iginla ya ce abun da ubangiji ya nuna masa tabbatacce ne kuma daya daga cikin alamomin zuwan karshen duniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

FCT, Abuja - Fasto Joshua Iginla na Champions Royal Assembly (Joshua Iginla Ministries), ya yi hasashen cewa tsakanin 2024 da 2026, mutane a fadin duniya za su fuskanci gagarumin sauyi a yanayin zafi da yanayi gaba daya.

Kara karanta wannan

Zanga-Zanga ta barke a sansanin NYSC na Abuja bayan soja ya lakadawa dan NYSC duka

Fasto Iginla, yayin wani taron coci na baya-bayan nan, ya ce koda dai yanayin zai sauya, hakan na "daya daga cikin alamomin zuwan karshen duniya".

Malamin addini ya yi hasashe kan 2024
“Alamomin Karshen Duniya”: Malamin Addini Ya Yi Hasashen Abun da Zai Faru a 2024 Hoto: Joshua Iginla Ministries
Asali: Facebook

Iginla ya yi hasashe kan 2024

Malamin addinin ya bayyana cewa "abubuwa da dama za su faru tsakanin yanzu da 2030."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalamansa:

"Tsakanin 2024 zuwa 2026, za ku ga wasu abubuwa da za su ba ku mamaki a sauyin yanayi kuma zai kasance mai karfi.
"Kimiyya za ta ba mu fassarar abin da suke tunani, amma an tsara wannan a matsayin daya daga cikin alamun karshen duniya.
“Ya kamata ku sani ba wai sambatu nake yi ba, kun san ina gani.
"Akwai wani wata da nake gani, 24, 25, 26, za ku fahimta. Akwai wani takamaiman wata da nake gani 9, 8, 11. Ku rubuta wannan rana, ku ajiye su, za ku ga wasu abubuwa.

Kara karanta wannan

"Za a yi bikin kirsimeti mai matukar hatsari", malamin addini ya yi hasashe kan Disamba

“Abubuwa da yawa za su faru tsakanin yanzu zuwa 2030.
"Za su taba zukatanku ta yadda za ku san cewa rubutun littafi gaskiya ne.
"Kimiyya za ta fassara abin da suke so su fassara. Amma ina gaya muku; shi ne alamun tashin duniya."

Kalli hasashen malamin a kasa:

Hasashe 50 game da 2024

A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa mani malamin addini, Apostle Chris Ajabor, ya yi hasashen cewa Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP a zaben 2023, zai bar Najeriya.

A hasashensa wanda ya wallafa a shafinsa na Facebook, Fasto Ajabor ya bayyana cewa Obi na shirin ficewa daga LP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng