Peter Obi Zai Yi Balaguro”: Malamin Addini Ya Yi Hasashen Abubuwa 50 da Za Su Faru a 2024

Peter Obi Zai Yi Balaguro”: Malamin Addini Ya Yi Hasashen Abubuwa 50 da Za Su Faru a 2024

  • Apostle Chris Ajabor, wanda ya kafa cocin Dr Apostle Chris Ajabor Ministries, ya yi hasashen cewa za a haifi jarirai da yawa a 2024
  • Malamin addinin ya bayyana cewa bam zai tashi a wani filin jirgin sama na kasa da kasa
  • Apostle Ajabor ya kuma yi hasashen cewa a 2024, za a fafata tsakanin coci da mutanen boye

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

FCT, Abuja - Wani malamin addini, Apostle Chris Ajabor, ya yi hasashen cewa Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP a zaben 2023, zai bar Najeriya.

A hasashensa wanda ya wallafa a shafinsa na Facebook, Fasto Ajabor ya bayyana cewa Obi na shirin ficewa daga LP.

Kara karanta wannan

"Za a yi bikin kirsimeti mai matukar hatsari", malamin addini ya yi hasashe kan Disamba

Malamin addini ya yi hasashen cewa Peter Obi zai yi kaura daga Najeriya
Peter Obi Zai Yi Balaguro”: Malamin Addini Ya Yi Hasashen Abubuwa 50 da Za Su Faru a 2024 Hoto: Mr. Peter Obi
Asali: Facebook

Manyan hasashe da Apostle Chris Ajabor ya yi game da 2024

Ajabor ya yi hasashen cewa za a kama wani shugaban kasa mai ci, yana mai cewa Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya, yana shirin barin PDP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duba hasashensa a kasa:

1. Za a haifi jarirai da yawa a shekarar 2024

2. Za a daure wani shugaban kasa mai ci

3. Za a fafata tsakanin coci da mutanen boye

4. Ku sayar da dalolin ku; yana shirin faduwa

5. Za a halatta auren jinsi daya a yawancin kasashen Kirista

6. Jirgin Air Peace Airline za su shiga matsala, amma Allah zai warware masu

7. Allah ya ji kanka baba...wani Janar na gab da tafiya makwanci

8. Peter Obi yana shirin ficewa daga Jam'iyyar LP

9. Fasto ABC ya fadi zabe

10. Na ga kasashe suna hadewa don zama kasa 1 mai karfi

Kara karanta wannan

Gagaruman abubuwa 3 da za su faru a 2024, malamin addini ya yi hasashe

11. Oduduwa zai fi Biyafara karfi a 2024

12. Za a kafawa sarakunan gargajiya sabuwar doka

13. Donald Trump a kan hanyar murna

14. Shirin hana Kesha (taron addu'an dare)

14. Minista Wike na shirin barin PDP

15. Ana shirin kaddamar da wani sabon kamfanin jirgin sama wanda zai gurgunta harkar sufurin jiragen sama

16. Matsala a ECOWAS

17. Ya kamata sshugabannin siyasar Kenya su yi taka-tsan-tsan don gujewa bala'i a kansu da al'ummar kasar

18. Julius Malama zai fadi zabe a Afrika ta Kudu

19. Allah zai kira fitattun shugabanni 3 (Na riga na sami sunaye da hotunanku)

20. Za a yi amfani da kudin Afirka daya amma yawancin kasashe za su ki amincewa da shi

21. Za a sanar da mutuwar wani tsohon shugaban kasa

22. Wani tsohon gwamna ya shirya zuwa gidan yari

23. Bam zai tashi a wani filin jirgin sama

Kara karanta wannan

Neman karbe kujerar Abba Gida-Gida a kotu zalunci ne kawai, Malamin Musulunci

24. Dr Chukwuemeka Okonkwo (E-money) ya yi hankali don gudun fitar da shi waje jinya

25. Wani Gwamnan Babban Bankin CBN...

26. Za a kama Simon Ekpa

27. Shugaban Afrika za su yi takaddama

28. Hatsarin jirgin kasa mafi girma a kasar Sin zai yi sanadin rasa rayuka

29. Dubai za ta yi alhini kan manyan abubuwan da za su faru

30. Za a dauke wuta a Mexico na kwanaki 4

31. Za a tilastawa Amurka yin amfani da janareta na lantarki

32. Batan jirgi

33. Mawakin duniya Flavor yana bukatar addu'ar mu

34. Fashewar gada

35. Tayar da matattu zai zama gama gari

36. Annabi Shepherd Bushiri yana bukatar addu'ar mu Ina hango wahala

37. Bacewar kudi (a zahiri)

38. Sabon kulle; wata babbar cuta

39. Za a soke Visa a wasu kasashen Turai

40. An hade coci 2

Kara karanta wannan

Da kamar wuya: Zai yi wahala Mmatatun Najeriya su yi aiki inji tsohon shugaban NNPC

41. Za a samu maganin Kanjamau

42. Za a kama wani shahararren marubucin yanar gizo kuma a yanke masa hukunci bisa laifin safara

43. Za a yi cinikin NTA (Nigeria)

44. Burna Boy ya koma gida yana murmushi

45. Ku taya baba Odinga (Kenya) da addu'a

46. ​​Wani tsohon gwamna zai rasa dansa

47. Ambaliyar ruwa a Ghana da Najeriya. Ba za a rasa rai ba

48. Tsohon gwamna Ifeanyi Okowa (jihar Delta) ya shirya ma matsala

49. Peter Obi zai yi kaura

50. Za a kama wata mai wa'azi kuma a kusan daureta idan ba a yi hankali ba

Fato ya yi hasashe kan zaben Kano

A wani labarin kuma, mun ji cewa Primate Babatunde Elijah Ayodele, shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual ya yi martani kan hukuncin da Kotun Koli za ta yanke a kan takkadamar zaben gwamnan jihar Kano.

Primate Ayodele ya bukaci dan takarar gwamna na jam'iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf, da ya ci gaba da neman taimakon Allah domin samun makoma mai kyau a Kotun Koli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng