Farfesa Yakubu Ya Rantsar da Sabbin Shugabannin INEC Na Jihohi 9, Ya Tsallake Guda Ɗaya
- INEC ta rantsar da sabbin kwamishinonin zaɓe 9 daga cikin guda 10 da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa
- Farfesa Mahmud Yakubu, wanda ya rantsar da su ranar Talata, ya ce za a rantar da ragowar ɗayan na jihar Akwa Ibom a 2024
- Ya gargaɗe su kan su yi aiki tukuru wajen gudanar da zaɓe sahihi kuma ingantacce tare da tuntuɓar juna a kai a kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC) ta rantsar da sabbin kwamishinonin zaɓe (REC) guda tara cikin 10 da Shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya naɗa.
Wannan ya biyo bayan tantance su da kuma amincewar da majalisar tarayya ta yi bayan fadar shugaban ƙasa ta miƙa mata.
Shugaban INEC na kasa, Farfesa Mahmud Yakubu ne ya rantsar da sabbin RECs ɗin a taron kwamishinonin zaɓe na jihohi wanda ya gudana ranar Litinin a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar INEC ta tabbatar da haka a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter a kwanakin baya.
Meyasa ba a rantsar da ragowar guda ɗaya?
Sanarwan ta ce kwamishinan da aka naɗa daga jihar Akwa Ibom ba ya cikin waɗanda suka karɓi rantsuwar kama aiki a yau Talata.
Yakubu ya yi bayanin cewa za a rantsar da shi a watan Janairu, 2023 bayan ƙarewar wa'adin wanda ke ci yanzu haka.
Shugaban hukumar ta INEC ya shaidawa RECs, musamman sabbin da aka nada cewa baya ga babba nauyin gudanar da zabe da ya hau kansu, ana buƙatar su yi sahihin aiki mai tsafta.
Yakubu ya ce:
"A matsayin ku na kwamishinonin zaɓe, ku ne wakilan Hukumar INEC a Jihohi daban-daban waɗanda za a tura ku nan ba da jimawa ba. Aikin hukumarmu ba ƙarami bane."
"Dole ne ku kiyaye al'adar hukumar zaɓe na tuntubar juna akai-akai tare da masu ruwa da tsaki masu mahimmanci a wuraren aikinku."
Jerin sunayen kwamishinonin da jihohin da aka tura su
Jim kaɗan bayan haka INEC ta tura dukkan kwamishinonin jihohin da zasu yi aiki, ga su kamar haka:
1. Abubakar Dambo Sarkin Pawa - Kebbi
2. Abubakar Ma’aji Ahmed - Borno
3. Dakta Anugbum Onuoha - Edo
4. Ehimeakhe Shaka Isah - Akwa Ibom
5. Mallam Aminu Idris - Kaduna
6. Mohammed Sadiq Abubakar - Kwara
7. Misis Oluwatoyin O. Babalola - Ondo
8. Olubunmi O. Omoseyindemi - Ekiti
9. Shehu L. Wahab - Nasarawa.
Tinubu ya tura sunayen kwamishinonin NPC ga majalisa
A wani rahoton na daban Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci majalisar dattawa ta amince da naɗin sabbin kwamishinonin hukumar kidaya ta ƙasa (NPC).
Shugaban ƙasar ya aike da sunayen mutum 19 da ƙarin wasu uku ga majalisar a wata wasiƙa da ya miƙa ranar Talata.
Asali: Legit.ng