Shugaba Tinubu Ya Aike da Sunayen Sabbin Kwamishinonin NPC 19 da Wasu Mutum 3 Ga Majalisar Dattawa
- Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci majalisar dattawa ta amince da naɗin sabbin kwamishinonin hukumar kidaya ta ƙasa (NPC)
- Shugaban ƙasar ya aike da sunayen mutum 19 da ƙarin wasu uku ga majalisar a wata wasiƙa da ya miƙa ranar Talata
- Sanata Akpabio ya miƙa aikin tantantance wa ga hukumar katin shaidar zama ɗan ƙasa (NIMS) domin ta kawo rahoto da wuri
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya aike da wasiƙa ga majalisar dattawan Najeriya kan naɗin kwamishinonin hukumar kidaya ta ƙasa (NPC).
A wasiƙar kamar yadda Channels tv ta ruwaito, Shugaban Kasar ya nemi sanatoci su amince da jerin sunayen mutum 19 da ya rubuto a matsayin kwamishinonin NPC.
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ne ya karanta sunayen da Bola Tinubu ya aiko a zaman majalisar na ranar Talata, 12 ga watan Disamba, 2023, The Cable ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jerin sunayen mutum 19 da Tinubu ya naɗa a matsayin kwamishinonin NPC
Legit Hausa ta tattaro muku jerin sunayen waɗanda Tinubu ya nemi amincewar majalisar dattawa domin naɗa su a wannan muƙami, ga su kamar haka:
1. Emmanuel Eke (Abia)
2. Clifford Zirra (Adamawa)
3. Chidi Ezeoke (Anambra)
4. Isa Buratai (Borno)
5. Alex Ukam (Kuros Riba)
6. Blessyn Brume-Ataguba (Delta)
7. Jeremiah Nwankwegu (Ebonyi)
8. Tony Aiyejina (Edo)
9. Ejike Ezeh (Enugu)
10. Abubakar Damburam (Gombe)
11. Uba Nnabue (Imo)
12. Dogon Garba (Kaduna)
13. Aminu Tsanyawa (Kano)
14. Yori Afolabi (Kogi)
15. Olakunle Sobukola (Ogun)
16. Temitayo Oluwatuyi (Ondo)
17. Mary Afan (Filato)
18. Ogiri Henry (Ribas)
19. Saany Sale (Taraba)
Bugu da ƙari, Tinubu ya buƙaci majalisar ta tantance tare da tabbatar da naɗin Bashir Indabawa (Arewa maso Yamma), Enorense Amadasu (Kudu maso Kudu) da Babajide Fasina (Kudu maso Yamma) a matsayin kwamishinonin NPC.
Majalisar karkashin Sanata Akpabio ta mika sunayen ga hukumar katin shaida ta kasa (NIMC) kuma ta nemi kawo rahoto cikin mako biyu.
Peter Obi ya kai ziyara Kaduna
A wani rahoton kuma Peter Obi ya bayyana matsalar da aka samu tun farko kan yawaitar kuskuren jefa wa fararen hula bam a Najeriya.
Ɗan takarar shugaban kasa na LP ya kuma bada shawarin mafita yayin da ya ziyarci waɗanda harin Tudun Biri ya shafa a Kaduna.
Asali: Legit.ng