Peter Obi Ya Dira Kaduna Kan Kisan Musulmai a Bikin Maulidi, Ya Faɗi Matsalar da Aka Samu Tun Farko

Peter Obi Ya Dira Kaduna Kan Kisan Musulmai a Bikin Maulidi, Ya Faɗi Matsalar da Aka Samu Tun Farko

  • Peter Obi ya bayyana matsalar da aka samu tun farko kan yawaitar kuskuren jefa wa fararen hula bam a Najeriya
  • Ɗan takarar shugaban kasa na LP ya kuma bada shawarin mafita yayin da ya ziyarci waɗanda harin Tudun Biri ya shafa a Kaduna
  • Ya bukaci gwamnatin tarayya ta samar da isassun kuɗi domin inganta ayyukan sojoji da sauran hukumomin tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Ɗan takarar shugaban kasa na Labour Party a zaɓen 2023, Peter Obi, ya roƙi gwamnatin tarayya ta gudanar da bincike kan kuskuren jefa bam a kauyen Tudun Biri.

Peter Obi ya ziyarci musulman da sojoji suka jefa wa bam a Kaduna.
Peter Obi Ya Ziyarci waɗanda harin sojoji ya shafa a Kaduna, ya nemi a yi bincike Hoto: Peter Obi
Asali: Facebook

Mista Obi ya kuma bukaci FG ta ƙara samar da isassun kuɗaɗe ga sojoji da sauran hukumomin tsaro domin kara inganta ayyukansu.

Kara karanta wannan

Mummunan hatsari ya laƙume rayukan aƙalla mutane 10 a babban titi a Najeriya

Ya yi wannan roko ne biyo bayan ruwan bama-baman da sojoji suka yi kwanan nan kan taron Musulmai a kauyen Tudun Biri, ƙaramar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon gwamnan jihar Anambra ya ziyarci waɗanda harin sojojin ya shafa a asibitin Barau Dikko ranar Talata, 12 ga watan Disamba, cewar rahoton The Nation.

Peter Obi ya yi ikirarin cewa sau 16 kenan sojoji na yin kuskuren jefa wa fararen hula bam a faɗin ƙasar nan, wanda ya yi sanadin kashe mutane sama da 500.

Gwamnati ce ta yi sake tun farko - Obi

Ya bayyana cewa babbar matsalar da aka samu tun farko shi ne babu abinda gwamnatin tarayya ke yi domin magance faruwar irin haka a gaba.

Domin hana afkuwar lamarin nan gaba, tsohon gwamnan ya bukaci gwamnati da ta taimakawa sojojin kasar da isassun kayan aiki.

Kara karanta wannan

Harin bam kan masu Mauludi: CDS ya nemi afuwar yan Najeriya, ya yi muhimmin alkawari 1

A rahoton Channels tv, Obi ya yi nuni da cewa, magance matsalolin tsaro da ake fuskanta a yanzu da kuma nan gaba na bukatar isassun kayan aiki ga sojojin kasar nan.

Ya goyi bayan kafa wata gidauniya ta musamman da za ta tallafa wa wadanda harin Tudun Biri ya rutsa da su, musamman waɗanda suka zama marayu.

Wani Mummunan Ibtila'i Ya Halaka Akalla Mutum 10

A wani rahoton na daban Akalla mutane 10 sun mutu a mummunan ibtila'in hatsarin mota da ya rutsa da su a babban titin Legas zuwa Ibadan.

Haɗarin wanda ya auku da karfe 5:00 na asuba sakamakon gudun wuce ƙima ya kuma bar ƙarin wasu fasinjoji 7 kwance a asibiti.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262