Mummunan Hatsari Ya Laƙume Rayukan Akalla Mutum 10 a Babban Titi a Najeriya
- Akalla mutane 10 sun mutu a mummunan ibtila'in hatsarin mota da ya rutsa da su a babban titin Legas zuwa Ibadan
- Haɗarin wanda ya auku da karfe 5:00 na asuba sakamakon gudun wuce ƙima ya kuma bar ƙarin wasu fasinjoji 7 kwance a asibiti
- Kwamandan hukumar kiyaye haɗurra a jihar Ogun ya yi takaicin abinda ya faru, a cewarsa za a iya guje wa hatsarin da an bi ƙa'ida
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ranar Talata ta zama wata baƙar rana ga iyalan wasu fasinjoji yayin mummunan hatsari ya rutsa da motoci biyu a kan babban titin Legas zuwa Ibadan, jihar Oyo.
Channels tv ta rahoto cewa hatsarin wanda ya auku da misalin karfe 5:00 na asubahi ya yi ajalin akalla mutane 10 da ke cikin motocin biyu.
Bayanai sun nuna cewa motocin biyu sun yi hatsari ne a daidai wurin kwana na Kara da ke kan babban titin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jami'ar hulda da jama'a ta hukumar kiyaye haɗurra ta kasa (FRSC) reshen jihar Ogun, Florence Okpe, ta tabbatar da faruwar lamarin.
A cewarta, bayan waɗanda suka rasa rayukansu, ƙarin wasu fasinjoji bakwai sun samu raunuka daban daban.
Ta faɗi bayanan motocin biyu da hatsarin ya rutsa da su, wanda suka ƙunshi, mota kirar Toyota Hiace Bus mai launin toka da lamba FKY898YF; da Iveco Truck Tipper mai launin ƙwai.
Yadda motocin suka gamu da hatsarin
Kakakin FRSC ta jihar ta ƙara da bayanin cewa mutane 18 duk maza ne hatsarin ya rutsa da su, wanda ake zargin gudun wuce ƙima ne ya haddasa shi.
An tattaro cewa diraban motar Bas ɗin ne ya gaza riƙe motar saboda tsakanin gudu, inda ya bugi babbar motar tifa wacce ke kokarin yin kwana ta canza hannu.
A ruwayar Daily Post, Okpe ta ce:
“An kai wadanda suka jikkata zuwa asibitin Famobis domin kula da lafiyarsu, yayin da aka ajiye gawarwakin a ɗakin ajiyar gawa na Idera Morgue, Sagamu."
"Kwamandan hukumar FRSC mai kula da yankin, Anthony Uga, ya ji raɗaɗin aukuwar mummunan hadarin wanda za a iya kauce masa idan da an yi taka tsantsan."
"Ya kuma jaddada cewa ya kamata direbobi su riƙa hutun mintuna 15 a kowane tukin sa’o’i hudu domin gajiya ke haddasa mafi akasarin hatsarin ababen hawa."
Yan bindiga sun ƙara shiga Abuja
A wani rahoton kuma Ƴan bindiga sun sake kai hari wani ƙauye a babban birnin Abuja, sun kashe jami'in tsaro tare da sace wasu mutum 12.
Mazauna yankin sun ce yan banga sun yi kokarin daƙile harin amma 'yan bindigan suka ci ƙarfinsu da makamai.
Asali: Legit.ng